Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta Kan Matafiya, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Yawa

Yan Bindiga Sun Buɗe Wuta Kan Matafiya, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Yawa

  • Wasu ƴan bindiga sun yi awon gaba da matafiya 18 da direban mota a a jihar Akwa Ibom da ke shiyyar Kudu maso Kudu
  • Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Timfon John ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami'an tsaro sun fara bincike
  • Wata majiya da ta nemi a sakaya bayananta ta ce ƴan bindigar sun tare motar bayan sun buɗe wuta, suka tasa mutanen da ke ciki zuwa jeji

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Anambra - Wasu miyagun ƴan bindiga sun yi garkuwa da direban mota da fasinjoji 18 a jihar Akwa Ibom da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

Lamarin ya faru ne a makon jiya a kan bodar Azumini tsakanin jihohin Akwa Ibom da Abia.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai mummunar hari a Zamfara, mutum 4 sun mutu yayin da aka sace 150

Yan sandan Najeriya.
Yan bindiga sun sace direba da fasinjoji 18 a jihar Akwa Ibom Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Channels tv ta tattaro cewa motar bas din ta bar tashar Uyo ta wuce Iwukem a karamar hukumar Etim a jihar Akwa Ibom, kafin ƴan bindigar su tare ta a yankin Azumini.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda 'yan bindiga suka sace matafiya 19

Wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta ce ‘yan bindigar sun tare direban bas din ne bayan sun buɗe wuta, daga bisani wasu ƴan uwan maharan suka fito daga jeji.

Majiyar ta kara da cewa maharan sun umurci dukkan fasinjojin su fito daga cikin motar ko kuma su harbe mutum har lahira idan ya tsaya gardama.

"Direban ne ya fara saukowa, daga bisani suka tilasta wa fasinjojin, kowa ya fito daga motar, suka tasa su zuwa cikin jeji, har yanzu babu wanda ya san inda suka yi," in ji shi.

Wane mataki ƴan sanda suka ɗauka?

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga taron FEC a Aso Rock, an yi shirun minti 1 saboda mutuwar Jigo

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom, ASP Timfon John, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin wata tattaunawa ta wayar tarho yau Talata.

A rahoton Vanguard, kakakin ƴan sandan ya ce:

“Rundunar ‘yan sandan jihar tana da masaniya kuma a yanzu tana ci gaba da sanya ido kan lamarin.
“Lamarin ya faru ne a yankin Azumini da ke kan titin bayan wuce karamar hukumar Etim Ekpo. Abin da zan iya cewa shi ne ‘yan sanda na ci gaba da aiki kan lamarin a yanzu."

DSS ta gano gidan mai taimakawa ƴan bindiga

A wani labarin kun ji cewa Dakarun hukumar DSS sun kai samame gidan wani ɗan adaidaita sahu da ake zargin yana da alaƙa da ƴan bindiga a jihar Neja.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an tsaron sun kwato makamai da kuɗaɗe ciki harda Daloli a gidan mutumin ranar Laraba da ta gabata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262