Sarautar Kano: Dan Agundi Ya Fadi Kuskuren da Aka Tafka a Nadin Sanusi II, Ya Jero Dalilai

Sarautar Kano: Dan Agundi Ya Fadi Kuskuren da Aka Tafka a Nadin Sanusi II, Ya Jero Dalilai

  • Sarkin Dawaki Babba, Baffa Dan Agundi ya bayyana kuskuren da aka yi tun farko kan mayar da Sanusi II sarauta
  • Dan Agundi ya ce mahaifin Sanusi II ba sarki ba ne domin haka bai kamata ya gaji kujerar sarauta a jihar Kano ba
  • Ya ce Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero shi ya cancanci kujerar saboda mahaifinsa Sarki ne har da kakanninsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Sarkin Dawaki Babba, Aminu Dan Agundi ya yi martani kan rigimar sarautar Kano.

Dan Agundi ya ce tun farko akwai babban kuskure wurin mayar da Muhammadu Sanusi II kan kujerar sarauta.

Baffa Dan Agundi ya yi martani kan sarautar Kano da mayar da Sanusi II
Baffa Dan Agundi ya bayyana kuskuren da aka yi tun farko game da mayar da Sanusi II sarauta. Hoto: @masarautarkano.
Asali: Twitter

Sarautar Kano: Dan Agundi ya gano matsala

Kara karanta wannan

Karshen tika tika: Kotu ta yanke hukunci kan dambarwar masarautar Kano

Sarkin Dawaki Babba ya bayyana haka ne yayin hira ta musamman da gidan talabijin na Arise a yau Talata 16 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dan Agundi ya ce Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero shi ne ya cancanci kujerar saboda gadonta ake yi.

Ya ce Sanusi II ne kaɗai ya gaji kujerar sarautar Kano duk da cewa mahaifinsa ba sarki ba ne fiye da shekaru 200 a tarihi.

Dan Agundi ya fadi kuskuren nadin Sanusi

"An riga an yi kuskure tun farko, nadin Muhammadu Sanusi II kan sarauta da aka yi tun farko an tafka kuskure kuma ba a bi ka'ida ba."
"Kujerar sarautar Kano gadonta ake yi, sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero shi ne ya cancanta saboda mahaifinsa Ado Bayero sarki ne da ya shafe fiye da shekaru 60 yana sarauta."

Kara karanta wannan

"Farar ƙafa": Ƙungiyar KYC ta faɗi abin da ya jawo gobara a fadar Sarkin Kano Sanusi II

"Kakanninsa sarakuna ne haka ma bangaren mahaifiyarsa ita ma ƴar sarki ne daga Ilorin a jihar Kwara."
"Mahaifin Sanusi Lamido ba sarki ba ne, fiye da shekaru 200 ba a taba samun irin abin da ya faru da Sanusi II ba a yanzu."

- Baffa Dan Agundi

Kotu ta raba gardama kan sarautar Kano

A wani labarin, kun ji cewa Babbar kotun jihar Kano ta raba gardama kan dambarwa da aka dade ana yi game da sarautar jihar.

Kotun ta dakatar da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna guda hudu ci gaba da kiran kansu sarakai a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.