Kano: Gwamna Abba Ya Ɗauki Muhimmin Matakin Kawo Ƙarshen Masu Ƙwacen Waya

Kano: Gwamna Abba Ya Ɗauki Muhimmin Matakin Kawo Ƙarshen Masu Ƙwacen Waya

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya dauki alkawarin kawo karshen kwacen wayaoyi da laifuka a kan tituna
  • Gwamnan ya bayyana cewa, zai inganta tsaro tare da tabbatar da kwato dukiyar talakawa da aka handame a fadin jihar
  • Ya mika godiyarsa ga jama'an ihar kan goyon bayan da suke ba shi a bikin ranar koyon sana'o'in matasa na duniya na 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya sha alwashin inganta halin da jama'a ke ciki, tabbatar da tsaro tare da kwato dukiyoyin al'umma a jihar Kano.

A jawabin gwamnan a ranar koyon sana'o'i ta matasan duniya a Kano na shekarar 2024, ya mika godiyarsa ga jama'an jihar Kano kan goyon bayansu da hadin kai.

Kara karanta wannan

Gwamnan Katsina ya bayyana hanyar da yake bi wajen samar da tsaro

Gwamnan Kano ya yi magana kan masu kwacen waya a kan tituna
Gwamna Abba Yusuf ya kafa rundunar hadin guiwa domin yaki da masu kwacen waya a Kano. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Gwamna Abba ya yi alkawarin inganta rayuwar dukkan 'yan jihar inda ya jaddada amfanin ilimi da kuma tsaro kamar yadda mai tallafa masa, Abdullahi I. Ibrahim ya sanar a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna ya yabawa gudumawar da jam'iyyar NNPP take bayarwa tare da godiya ga 'yan kasuwa, shugabannin addini da masarautun gargajiya.

Ya gode musu kan rawar da suke takawa wurin tabbatar da zaman lafiya da daidaito, yayin da ya yi maraba da zuwan baki daga sama da kasashe 20 na duniya.

"Za mu magance kwacen waya" - Gwamnan Kano

Domin inganta tsaro a kan titunan jihar, Gwamna Yusuf ya sanar da kafa rundunar hadin guiwa ta musamman domin yaki da masu kwacen waya.

Ya jadadda bukatar kwato kadarorin al'umma da aka barnatar tare da yin alkawarin bincike kan hargitsin siyasa da ta kawo rashe-rashen rayuka da kadarori a fadin jihar.

Kara karanta wannan

Ruwa ya ruguza gidaje da rumbunan abinci a Arewa, mutane sun shiga tasko

Jawabin gwamnan ya bayyana irin mayar da hankalin da mulkinsa yayi wurin ganin zaman lafiya da cigaban jihar Kano, tare da tabbatar da makoma mai kyau ga jama'an jihar.

An caccaki Abba Gida-gida da Kwankwaso

A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa, sakamakon shari'a kan dambarwar sarautar Kano ta jawowa Gwamna Abba Kabir Yusuf da jagora Rabiu Musa Kwankwaso suka.

Wata kungiya mai zaman kanta a jihar Kano, ta bayyana cewa an nuna son kai karara a hukuncin kuma wannan abin kunya ne.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.