'Yan Bindiga Sun Kai Mummunar Hari a Zamfara, Mutum 4 Sun Mutu Yayin da Aka Sace 150

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunar Hari a Zamfara, Mutum 4 Sun Mutu Yayin da Aka Sace 150

  • Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki da tsakar rana a kauyen Dan Isa dake karamar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara
  • An ce 'yan bindigar sun isa kauyen a kan babura kusan 150 inda suka halaka rayuka hudu tare da yin garkuwa da wasu mutane 150
  • Daga cikin wadanda suka yi garkuwa dasu akwai yara na goye, 'yan watanni shida da takwas tare da iyayensu mata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Zamfara - 'Yan bindiga sun halaka mutane hudu tare da yin garkuwa da wasu mutum 150, ciki har da jarirai 'yan watanni shida da takwas.

Wannan ya faru ne a farmakin da miyagun suka kai kauyen Dan Isa dake karamar hukumar Kauran Namoda a jihar Zamfara a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro a Abuja: Ƴan bindiga sun harbi jigon APC, sun tafi da mutane 5

'Yan bindiga sun kai farmaki jihar Zamfara
'Yan bindiga sun kashe mutum 4, sun tafi da wasu 150 a harin da suka kai Zamfara. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Dan Isa na nan a kusa da Gusau, babban birnin jihar Zamfara. Kauyen yana da nisan kilomita 14 daga babban birnin, Daily Trust ta bayyana haka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan farmakin na zuwa ne mako daya bayan da 'yan bindiga suka sako mazauna yankin Dogon Kade 46 bayan an biya kudin fansa da ya kai Naira miliyan 21.

Zamfara: 'Yan bindiga sun sace jarirai

Wani mazaunin Dan Isa, wanda aka sace matarsa da dansa, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Mazaunin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce 'yan bindigan sun tsinkayi kauyen wurin karfe 3 na tsakar ranar Lahadi kuma sun kwashi awanni shida suna barna.

"Matata, Na'imah da jaririnmu Sudai mai watanni shida suna daga cikin wadanda aka sace. Matar dan uwana, Aisha da jaririnta mai watanni takwas duk an sace su."

Kara karanta wannan

Takun saƙar Wike da Fubara: Jigon PDP ya faɗi hanyoyi 4 na magance rikicin Rivers

- A cewar mazaunin kauyen.

An sace matar Wamban Dan Isa

Wani mazaunin yankin, Muhammad Auwal, ya ce Hajiya Rakiya, matar Wamban Dan Isa, Alhaji Bello Halilu, na daga cikin matan da aka sace kuma an raunata wasu a gidan Halilu.

Matan kanin Wamban Dan Isa, Malama Luba da Malama Talatu suna cikin wadanda aka yi garkuwa da su, kamar yadda Malam Auwal ya bayyana.

Malam Auwal ya ce:

"Na gano cewa Malam Musa Ajiya yana daga cikn wadanda suka arce daga hannun 'yan bindigan amma mata hudu har da matarsa da matar kaninsa an tafi da su.

Yaran Bagiwa ne suka kai harin

Aminu Bello Dan Isa, wani mazaunin yankin, ya ce kungiyar ta'addancin karkashin jagorancin Alhaji Shehu Bagiwa ne suka kai farmakin.

Duk da majiyoyi sun tabbatar cewa babu Bagiwa cikin harin kai tsaye, matan da suka tsere sun ga babban yaronsa, Aminu Baka-da-dadi, yana jagorantar harin.

Kara karanta wannan

Kamar al'amara: Yadda barawo ya yaudari direban kabu-kabu da farfesa, ya sace motarsa

Tuni jama'a suka tattara komatsansu suka bar kauyen suka koma wurare kamar Kasuwar Daji, Rawayya, Gyambarawa da Gusau, saboda tsoron cigaban farmakin.

'Yan bindiga sun shiga Abuja

A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa 'yan bindiga sun kai farmaki Yangogi dake yankin Kwali a babban birnin tarayya.

Sun shiga gidan jigon jam'iyyar APC inda suka harbe shi tare da tasa keyar yaransa guda biyu da wasu makwabtansa uku.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.