'Yan Damfara Sun Yiwa Lambar Wayar Gwamna a Najeriya Kutse, an Gargadi Mutane
- Hankula sun tashi a Osun bayan ƴan damfara sun yi kutse a lambar wayar Gwamna Ademola Adeleke a jiya Litinin 15 ga watan Yulin 2024
- Gwamnatin jihar ta sanar da cewa an yi kutsen ne a lambar wayar gwamnan kamar haka: +234 803 365 7555 inda ta gargadi mutane
- Kakakin gwamnan jihar, Mallam Olawale Rasheed shi ya tabbatar da haka inda ya gargadi jama'a da su yi hankali wurin mu'amala da lambar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Osun - Gwamnatin jihar Osun ta sanar da cewa ƴan damfara sun yi kutse a wayar Gwamna Ademola Adeleke.
Gwamnatin jihar ta yi gargadi cewa kowa ya yi hankali da duk wani sako daga lambar wayar kamar haka: +234 803 365 7555.
Ƴan damfara sun kwace iko da wayar Gwamna
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Mallam Olawale Rasheed ya fitar, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olawale Rasheed ya bukaci al'umma da su yi hankali da duk wani taimako da za a bukata daga lambar wayar Gwamna Ademola Adeleke.
Ya ce hukumomi suna iya bakin kokarinsu wurin tabbatar da shawo kan lamarin cikin gaggawa ba tare da an cutar da kowa ba, Punch ta tattaro.
"Muna kira ga al'umma kowa ya yi hankali da duk wani taimako ko bukata daga wannan lambar waya: +234 803 365 7555."
"Hukumomi na kokarin daukar matakai domin shawo kan matsalar cikin gaggawa."
- Mallam Olawale Rasheed
Gwamnatin Osun ta shawarci al'umma
Gwamnatin jihar ta bukaci al'umma da su kwantar da hankali tare da saka ido domin zakulo wadanda suka aikata hakan.
Ta yi alkawarin ci gaba da sanar da al'umma halin da ake cikin da sa ran an samu wani ci gaba dangane da hakan.
An yi kutse a lambar Gwamna Otu
Kun ji cewa Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu ya shiga matsala bayan ‘yan damfara sun yi nasarar yin kutse a lambar wayarsa.
‘Yan damfarar tuni suka fara neman taimakon kudade daga jama’a wadanda kaddarar ta fada kansu inda gwamnatin ta tura gargadi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng