Ana Shirin Zanga Zanga, Gwamnati Ta Yi Albishir, Ta Fadi Lokacin Saukar Farashin Abinci

Ana Shirin Zanga Zanga, Gwamnati Ta Yi Albishir, Ta Fadi Lokacin Saukar Farashin Abinci

  • Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta yi albishir ga yan Najeriya kan cewa farashin kayan abinci zai sauko kasa ba da dadewa ba
  • Karamin ministan noma, Aliyu Abdullahi ya bayyana cewa a yanzu haka an riga an dauki matakan da za su sauko da farashin abinci
  • Legit ta tattauna da Ibrahim Sale Aliyu kan jin yadda ya dauki alkawarin gwamnatin na samun saukin farashin abinci nan kusa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta yi albishir ga yan Najeriya kan saukar farashin kayan masarufi a fadin ƙasar nan.

Albishir din na zuwa ne bayan gwamnatin ta amince da cewa a yanzu haka akwai karancin abinci a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Sadaukar da rabin albashi: 'Yan Najeriya sun aika sako ga 'yan majalisar wakilai

Kayan abinci
Gwamnati ta yi bayani kan saukar farashin abinci. Hoto: Bloomberg
Asali: Getty Images

Ƙaramin ministan harkokin noma, Aliyu Abdullahi ne ya yi albishir din a yau Litinin kamar yadda rahoton Channels Television ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tashin farashin kayyakki a Najeriya

Rahotan da cibiyar kididdiga ta NBS ta fitar ya nuna cewa an samu hauhawar farashin kayyakki da kashi 40% cikin watannin nan.

Masana sun bayyana cewa hakan ne ya sanya farashin kayan abinci ya tashi sosai inda talakawa suke kuka kan lamarin.

Gwamnatin Tinubu ta dauki mataki

Karamin ministan noma, Aliyu Abdullahi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kammala daukan matakai domin saukaka lamarin.

Aliyu Abdullahi ya bayyana cewa nan da kwanaki kadan yan Najeriya za su fara gani a kasa, rahoton Punch.

Wasu matakai aka dauka kan tsadar abinci?

Karamin ministan ya bayyana cewa a shekarun baya ba a cika ba harkokin noman rani muhimmanci sosai ba a Najeriya.

Kara karanta wannan

Majalisa na shirin kawo tsarin da zai ba Tinubu damar zarce shekara 4 ba tare da zabe ba

Amma a yanzu ya tabbatar da cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta ba bangaren muhimmanci sosai kuma za a ga amfanin hakan wajen kawo saukin farashin abinci.

Legit ta tattauna da Ibrahim Sale

Legit ta tattauna da Ibrahim Sale kan yadda ya dauki alkawarin da gwamnatin ta yi ga yan Najeriya.

Ibrahim Sale ya ce lallai an dade ana ruwa kasa na shanyewa kuma ba su zaton za a samu sauki idan dai daga maganar da gwamnati ta yi ne.

Farashin abinci ya fara sauka

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake fama da tsadar kayayyaki musamman bangaren abinci, an fara samun sauki a wasu jihohin Arewacin Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa jihohin da aka samu saukin idan aka kwatanta da kwanakin baya sun hada da Gombe da Jigawa da kuma jihar Bauchi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng