Ruwa Ya Ruguza Gidaje da Rumbunan Abinci a Arewa, Mutane Sun Shiga Tasko

Ruwa Ya Ruguza Gidaje da Rumbunan Abinci a Arewa, Mutane Sun Shiga Tasko

  • A yayin da damunar bana ke cigaba da kankama a jihohin Arewa an samu mamakon ruwa da ya yi gyara a jihar Adamawa
  • Rahotanni sun nuna cewa ruwan ya ruguza gidaje da dukiyoyi da dama yayin da aka ɗauki lokaci mai tsawo ana yinsa
  • Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya ziyarci wurin tare da yin alkawuran taimakawa mutanen garin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Adamawa - An samu mamakon ruwan sama da ya yi barna sosai ciki har da ruguza gidaje da dama a jihar Adamawa.

Rahotanni na nuni da cewa ruwan ya jawo asarar dukiya mai dimbin yawa ga wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna ya bayyana babbar matsalar Najeriya da Tinubu ya fara magancewa

Jihar Adamawa
Gidaje sun rushe sakamakon ruwan sama a Adamawa. Hoto: Adamawa State Planning Commission
Asali: UGC

Hukumar kula da tsare-tsaren gari a jihar ta wallafa a shafinta na yanar gizo cewa gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri ya ziyarci wajen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ruwa ya ruguza gidaje Michika

Gwamnatin jihar Adamawa ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a garin Blabiri a karamar hukumar Michika, rahoton Daily Trust.

Ta kuma tabbatar da cewa an samu asarar dukiya mai dimbin yawa wacce ta haɗa da lalacewar abinci, rugujewar gidaje da sauransu.

Bayan haka, gwamnatin ta kara da cewa ruwan saman ya jawo mutane da dama sun rasa sana'o'insu kasancewar barnar ta shafi wuraren da suke aiki.

Gwamnan Adamawa ya ziyarci Blabiri

Gwamna jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ziyarci garin Blabiri domin ganewa idonsa irin barnar da ruwan ya yi.

Gwamnan ya yi alƙawarin cewa gwamnatin za ta mika kayan tallafi domin rage radadi ga wadanda abin ya shafa.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta dauki mataki bayan gano masu ɗaukar makamai, su aikawa miyagu

Ya kuma shawarci wadanda suke kusa da tafki a garin da su nemi gidaje a gefe domin kaucewa fadawa cikin hadarin a gaba.

NEMA ta ba mazauna Legas shawara

A wani rahoton, kun ji cewa yayin da ake tsaka da fama da ambaliyar ruwa a Lagas, an bukaci mazauna jihar da su dauki matakan kariya cikin gaggawa.

Rahotanni sun nuna cewa hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa (NEMA) ce ta bayar da shawarar ga al'umma tare da bayyana irin matakan da ya kamata a dauka.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng