Ranar Ashura: An Tsananta Tsaro a Kaduna, Ƴan Sanda Sun Haramta Taron Ƴan Shi’a

Ranar Ashura: An Tsananta Tsaro a Kaduna, Ƴan Sanda Sun Haramta Taron Ƴan Shi’a

  • Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta sanar da haramta duk wani nau'in zanga-zanga ko tattaki da 'yan Shi'a ke shirin yi
  • Kakakin rundunar na jihar, ASP Mansir Hassan, ya ce sun samu bayanai cewa za ayi tattakin ranar Ashura da ya saba doka
  • ASP Hassan ya sanar da cewa, rundunar za ta dauki mataki a kan duk wanda yayi kunnen ƙashi kan wannan gargadi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kaduna - Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta ce ta haramta duk wani nau'i na taruka ba bisa ka'ida ba wanda kungiyar Shia'a ke gudanarwa ciki har da da tattakin ranar Ashura.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Kaduna.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi luguden wuta kan ƴan ta'adda a Arewa, sun faɗi nasarar da aka samu

Yan sanda sun yi magana kan tattakin 'yan Shi'a a Kaduna
Rundunar 'yan sanda ta haramta tattakin Ashura a jihar Kaduna. Hoto: UGC
Asali: UGC

An haramta tattakin Ashura a Kaduna

Jaridar Vanguard ta ruwaito ASP Hasssan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Rundunar ta haramta kowanne irin nau'in zanga-zanga ba bisa ka'ida ba a jihar. Bayanan sirri sun nuna cewa kungiyar 'yan Shi'a sun shirya tattaki domin bikin ranar Ashura.
"Sanin kowa ne cewa irin wannan tattakin yana kawo tashin hankali da tarzoma wanda a karshe ke jawo asarar dukiyoyi, raunuka da ma rasa rayukan jama'a.
“Wannan yana daga cikin abin da 'yan sandan ke jan kunnen kungiyar a kai, wanda tuni doka ta bukaci da su ajiye batun tattakin nan."

'Yan sanda sun gargadi 'yan Shi'a

ASP Hassan ya ce rundunar ba za ta yi kasa a guiwa ba wurin tabbatar da doka kan duk wani mutu ko kungiya, musamman 'yan Shi'a da suka ce zasu take haramcin gangamin.

Jaridar The Punch ta ruwaito ASP Hassan ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, Ali Dabigi, ya yi kira ga dukkanin jama'a da su cigaba da harkokinsu ba tare da fargaba ba.

Kara karanta wannan

Kamar al'amara: Yadda barawo ya yaudari direban kabu-kabu da farfesa, ya sace motarsa

CP Ali Dabigi ya kara da cewa, zaman lafiyan da aka samu a jihar ba zai gurbata ba ta hanyar taurin kan wasu mutane kadan.

An hallaka 'yan shi'a a Kaduna

A wani labari na daban, kungiyar 'yan shi'a da ke Kaduna ta bayyana cewa 'yan sanda sun halaka musu mambobi har hudu a arangamar da suka gwabza.

Aliyu Tirmizi, daya daga cikin manyan jagororin kungiyar ya ce suna tsaka da zanga-zangar lumana ne 'yan sanda suka afka musu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.