Muzaharar Ashura ta yan Shi'a ta rikide zuwa rikici a Sakkwato birnin Shehu

Muzaharar Ashura ta yan Shi'a ta rikide zuwa rikici a Sakkwato birnin Shehu

  • Rikici ya barke yayin taron muzaharar Ashura a jihar Sokoto
  • Yan Shi'a sun yi ikirarin cewa an kashe musu yan'uwa da an jikkata wasu
  • Yan sanda sun ce an kwantar da kura yanzu kuma komai ya lafa

Sokoto - Rikici ya barke tsakanin 'yan uwa mabiya akidar Shi'a da jami'an hukumar yan sanda a cibiyar daular Usmaniyya yayin Muzaharar ranar Ashura da akayi ranar Alhamis.

BBC ta ruwaito yan Shi'an da cewa yan sanda ne suka bude musu wuta lokacin da suke muzaharar.

A cewarsu, sun kammala zagayensu kenan yan sanda suka biyosu a baya suka harba musu barkonon tsohuwa.

Sun kara da cewa wannan harbi yayi sanadiyyar mutuwan akalla mutum biyu yayinda da dama sun jikkata.

Daya daga cikin ya Shi'an, Sidi Mannir Mainasara, ya laburta cewa:

Kara karanta wannan

A karshe kungiyar Arewa ta bayyana wanda Boko Haram suke tsoro fiye da 'yan sanda da sojoji

"An zo wurin shafa addu'a ana jawabin kammala yan sanda sun biyomu baya sun yi harbin kan mai uwa da wabi."
"Mutum 15 sun rigamu gidan gaskiya, sannan 13 da mumunan raunuka, daga ciki akwai karaya."
Muzaharar Ashura ta yan Shi'a ta rikide zuwa rikici a Sakkwato birnin Shehu
Muzaharar Ashura ta yan Shi'a ta rikide Hoto: Yan Shi'a
Asali: Depositphotos

Yan sanda sun karyata maganar yan Shi'a

A cewar rahoton, hukumar yan sanda ta musanta wannan magana.

Hukumar yan sanda a jihar Sokoto tace da mutane unguwan Mabera yan Shi'a suka fara samun matsala kuma hakan yayi sanadin barkewar rikici.

Hakan ya sa suka kai dauki domin kwantar da kuran.

Kakakin yan sanda, ASP Sunusi Abubakar

"Yan sanda sun hanzarta lokacin da bayani ya riskesu an je kuma an yi kokarin ganin cewa wani abu bai faru ba inda akayi amfani da tiya gas aka koresu aka hana wannan tashin hankalin dake kokarin ya faru."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan sanda sun ceto mutum 12 da aka sace a Zamfara

"Tiya gas kawai akayi amfani da shi wannan yana daidai da dokar yan sanda wajen kwantar da tarzoma."

Asali: Legit.ng

Online view pixel