Ranar Ashura: ‘Yan Sandan Najeriya sun kama wasu ‘Yan Shi’a

Ranar Ashura: ‘Yan Sandan Najeriya sun kama wasu ‘Yan Shi’a

- 'Yan Sanda sun cafke wasu 'Yan Shi'a lokacin da su ke tattaki

- Rundunar 'Yan Sandan na zargin 'Yan Shi'an da tada hatsaniya

- Yanzu an mika 'Yan Shi'an wajen babban ofishin Jami'an tsaro

Ranar Ashura: ‘Yan Sandan Najeriya sun kama wasu ‘Yan Shi’a
Jami’an tsaro sun kama wasu ‘Yan Shi’a lokacin tattaki a Zaria
Asali: Original

Mun ji labari cewa ‘Yan Sanda sun damke wasu Mabiya Shi’a a Garin Zaria lokacin da su ka fito muzahara a jiya Alhamis. Wannan rana dai ita ce Ranar Ashura da ‘Yan Shi’a ke fita kan titiuna su ka tattaki.

Mutane 4 daga cikin ‘Yan Shi’an da su ka fita tattaki a Unguwar Muchiya da ke cikin Karamar Hukumar Sabon Garin Zaria a Jihar Kaduna sun shiga hannun Jami’an tsaro. Jaridar Daily Trust ta rahoto hakan jiya.

Wani babban Jami’in ‘Yan Sanda a Jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa sun yi ram da wasu ‘Yan Shi’a da aka kama a cikin Zaria bayan da su ka kai wa Jami’an tsaro hari a kan hanya.

KU KARANTA: Mabiya Shi’a za su yi muzahara a babban Birnin Najeriya

Sabo wanda yake magana da yawun ‘Yan Sandan Jihar Kaduna ya bayyana cewa ‘Yan Shi’an sun tare titi sannan kuma su ka rika kai wa Jami’an tsaro hari da jifa da gwafa tare da hana Jama’a sakat a Ranar Alhamis.

Yanzu dai an mika wadanda aka kama zuwa babban ofishin binciken ‘Yan Sanda na CID. Sabo yace aikin ‘Yan Sanda ne su kawo zaman lafiya don haka dole su takawa ‘Yan Shi’an burki domin an haramta tattalki.

‘Yan Sandan su na zargin Mabiya Shi’an da fasa wata motar su lokacin da su kayi jifa kan Jami’an tsaron. Dama dai jiya ne Mabiya Shi’an su ka shirya muzahara a babban Birane domin tunawa da Jikan Manzo Husseini.

Kwanaki kun ji cewa fitaccen Malamin addinin nan na Kaduna Ahmad Gumi ya ba mutanen Najeriya shawara game da shugabanci inda yace su zabi wanda ya san aiki a mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng