Rugujewar Gini Kan Dalibai: Gwamnatin Filato Ta Sanar da Ranakun Zaman Makoki

Rugujewar Gini Kan Dalibai: Gwamnatin Filato Ta Sanar da Ranakun Zaman Makoki

  • Gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku daga 13 ga Yuli zuwa 15 ga Yuli, 2024
  • A yayin zaman makokin, za a sauke dukkanin tutoci a jihar domin karrama wadanda ginin makaranta ya rufta a kansu a garin Jos
  • Akalla mutane 22 ne suka rasa rayukansu sannan wasu malamai da daliban makarantar da ke Busa Buji a karamar hukumar Jos ta Arewa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Filato - Gwamnatin jihar Filato ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku biyo bayan asarar rayukan da aka yi a ginin makarantar Saint Academy da ya ruguje a ranar Juma’a.

Akalla mutane 22 ne suka rasa rayukansu sannan wasu malamai da daliban makarantar da ke Busa Buji a karamar hukumar Jos ta Arewa suka samu raunuka a iftila'in.

Kara karanta wannan

Gwamna ya rufe makarantar sakandire bayan mutuwar ɗalibai 22, ya ɗauki mataki

Gwamnan Filato ya yi magana kan ginin da ya rufta a kan dalibai
Gwamnatin Filato ta ayyana zaman makoki na kwana 3 bayan gini ya furta kan dalibai. Hoto: @CalebMutfwang
Asali: Facebook

Gwamnati ta ayyana makoki a Filato

Dangane da hakan, gwamnati ta bayar da umarnin a sauke dukkan tutoci a jihar a zaman makoki na kwanaki uku da za a fara daga ranar 13 ga watan Yuli zuwa 15, inji rahoton Channels.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya fito ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar Filato Musa Ashoms a ranar Asabar.

Gwamna Caleb Mutfwang, wanda ya ziyarci makarantar a ranar Asabar, ya jajantawa iyalan da lamarin ya shafa inda ya bukaci al'ummar jihar da su rika kiyaye dokokin gini.

Gwamna ya ba masu gini sabon umarni

Ya jaddada bukatar dukkanin mamallakan kadarori da su mika zane da bayanan gininsu ga hukumarbunkasa birnare ta Jos (JMDB) domin tantance ingancinsu.

A cewar rahoton AIT, jihar za ta samar da ingantacciyar kulawar jinya ga wadanda suka jikkata kuma za ta gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin rugujewar ginin.

Kara karanta wannan

Mutum 22 sun mutu sakamakon mummunan ibtila'in da ya afka wa ɗalibai a Arewa

Gwamnan ya kuma bayyana cewa, tsaro da walwalar ‘yan kasa, musamman yara, shi ne babban fifiko a jihar, inda ya kuma bukaci dukkan makarantu da su bi ka’idojin kula da lafiya.

Gini ya rufta kan dalibai a Jos

Tun da fari, mun ruwaito cewa ginin wata makaranta ya rushe kan ɗalibai da ke tsakiyar rubuta jarabawa a Busa Buji da ke ƙaramar hukumar Jos a jihar Filato.

Rahotanni sun bayyana cewa iyayen yara sun garzaya wurin suna kukan neman agaji kuma tuni jami'an tsaro suka dura makarantar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.