Wahalar Fetur Za Ta Tsananta, Dillallan Mai Sun Shiga Yajin Aiki a Wasu Jihohin Najeriya
- Wani abu mai kama da yajin aiki ya faru a Oyo da Osun inda dillalan man fetur suka rufe gidajen mai a fadin jihohin biyu
- Kungiyoyin 'yan kasuwar man na IPMAN da NUPENG sun ce 'yan sanda sun matsawa mambobinsu da karbar kudi da cin zarafi
- A cewar 'yan kasuwan, ba za su bude gidajen main ba har sai an dakatar da 'yan sanda daga hantarar mambobinsu a manyan hanyoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Mambobin kungiyoyin dillalan man fetur na IPMAN da NUPENG a jihohin Oyo da Osun sun dakatar da aiki tare da rufe gidajen mansu.
Dillalan man, a wani taron gaggawa da suka gudanar a Ibadan ranar Asabar, sun ce sun yanke shawarar ne saboda “Karbar kudi da hantarar da ‘yan sanda ke yiwa mambobinsu."
IPMAN. NUPENG sun shiga yajin aiki
Taron ya samu halartar shugaban defo na Ibadan, Mutiu Bukola da Hammed Hamzat shugaban direbobin tankar man fetur (PTD) reshen kungiyar NUPENG, inji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Surajudeen Adegoke, shugaban kungiyar ‘yan kasuwar mai ta NUPENG, da Olalekan Lawal, mataimakin shugaban kungiyar IPMAN.
A cewar jaridar The Punch, sun yi Allah wadai da cin kashin da ‘yan tawagar sa ido na sufetan ‘yan sanda (IGP) suke yiwa mambobinsu a kan manyan hanyoyi.
Yaushe za a sake bude gidajen man?
Sun ce tsangamar da jami'an tsaron ke nunawa mambobinsu ne ya jawo babban gibi wajen dakon man fetur daga defo zuwa gidajen mai na fadin jihohin biyu.
Mista Bukola wanda ya yi magana a madadin kungiyoyin ya yi kira da a gaggauta kawo karshen cin zarafi da karbar kudaden da ake yi wa mambobin kungiyoyinsu.
Ya ce ba za su bude gidajen man ba ba har sai an magance matsalolin.
NNPC zai nemo sabon bashin $2bn
A wani labarin, mun ruwaito cewa kamfanin man fetur na Najeriya, NNPC ya fara shirin karbo sabon bashin $2bn da zai bashi damar tafiyar da ayyukansa.
Shugaban kamfanin, Mele Kyari ya bayyana hakan a yayin da rahotanni suka bayyana cewa NNPC na fuskantar matsin lamba sakamakon wahalar fetur ta tsananta.
Asali: Legit.ng