"Hana Makiyaya Kiwo a Sake Zai Jawo Manyan Matsaloli 3 a Ƙasa," KACRAN
- Masu ruwa da tsaki a bangaren kiwo a Najeriya na ta nuna illar kokarin da majalisa ke yi ka hana kiwo a sake
- Kungiyar makiyaya ta Kulen Allah cattle breeders association of Nigeria (KACRAN) na ganin dokar za ta haifar da matsaloli
- Shugaban kungiyar, Khalil Mohd Bello ya shaidawa Legit cewa idan kudurin ya zama doka, matsalolin da za a samu za su fi na baya yawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano - Batun haramta kiwon sake ga dabbobin makiyaya na yamutsa hazo tsakanin masu ruwa da tsaki a Najeriya. A ranar 5 Yuni, 2024, majalisar kasar nan ta dauki dumi bayan dan majalisa Titus Tartenger Zam daga jihar Binuwai ya gabatar da kudiri kan kiwon dabbobi.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Titus Tartenger Zam na ganin cewa rashin dokar hana kiwo a sake na jawo fadan manoma da makiyaya.
"Dokar za ta jawo matsaloli," KACRAN
Yan majalisa, musamman na Arewacin kasar nan na ganin dokar hana kiwo a sake ba ta da amfani, kamar yadda Arise Television ta wallafa. A wannan rahoton, kungiyar makiyaya ta Kulen Allah cattle breeders association of Nigeria (KACRAN), ta shaidawa Legit manyan illoli uku da kudurin zai haifar idan ya zama doka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jerin matsalolin da hana kiwo a sake zai haifar a Najeriya;
1. Tauye hakkin motsawa ga Fulani
Shugaban KACRAN, Khalil Mohd Bello ya bayyana cewa hana Fulani kiwo da dabbobinsu a sake ya tauye masu hakkin motsawa a matsayinsu na 'yan kasa.
Ya ce duk da kokarin dan majalisa mai wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Muhammad Adamu Aliero na bayyana hakan, da yawa ba a fahimce shi ba.
2. Karuwar rashin tsaro
Shugaban KACRAN ya ce hana motsawa daga yankunan Arewa zuwa Kudancin kasar nan da ke da abincin dabbobi da ruwa zai kara jawo rashin tsaron rayukan dabbobin da Fulani. Shugaban ya buga misali da abin da ya faru a Binuwai inda aka haramta kiwon a sake tare da cin tarar makiyaya N27m. Ya ce bayan an dauki shanun a motoci zuwa Nasarawa ne jirage su ka budewa makiyan da dabbobinsu wuta.
3. Raguwar madara da nama
Shugaban KACRAN ya ce akwai babbar barazana ga bangaren samar da madara da nama matukar aka hana kiwo a sake. Khalil Mohd Bello ya ce abinci da dausayin da ke Kudancin kasar nan na taimakawa dabbobi sosai. A cewarsa, babu dabbobin da za su iya cinye dukkanin albarkar ciyayi da ke Kudu, kuma idan dabbobinsu sun kiwatu, karin abinci ne ga kasa.
An gano dalilin wariya ga Fulani
Khalil Mohd Bello ya ce ayyukan wasu Fulani 'yan bindiga na daga abubuwan da ya sa ake nuna kiyayya ga Fulani a Arewa da sauran sassan kasa.
Sai dai ya bayyana cewa da yawa daga Fulanin da su ka rikide zuwa 'yan ta'adda ba su da shanu, ba makiyaya ba ne.
Ya shawarci majalisar dokokin kasar nan ta yi abin da ya dace wajen samawa 'yan kasa sassauci maimakon daukar matakin kara yamutsa lamari.
Sanatoci sun yi sabani kan dokar kiwo
A baya mun kawo labarin cewa sanatoci daga Arewacin kasar nan sun ki amincewa da dokar hana makiyaya kiwo a sake.
Dan majalisar APC mai wakiltar Binuwai ta Tsakiya, Titus Tartenger Zam ne ya gabatar da kudirin, kuma har ya tsallake karatu na biyu.
Asali: Legit.ng