Allah Mai Yadda Ya So: Bidiyon haduwar Umar Bush da Dangote a Villa Ya Girgiza Jama’a

Allah Mai Yadda Ya So: Bidiyon haduwar Umar Bush da Dangote a Villa Ya Girgiza Jama’a

  • Umar Bush, wani dan Arewa da ya shahara wajen dura ashariya da fushi a kafar sada zumunta na ci gaba da samun shiga karkashin manya a Najeriya
  • A kwanakin nan bidiyonsa ya yadu, inda aka ga yadda aka gayyace shi zuwa fadar shugaban kasa, ya gamu da manyan kasar nan da yawa
  • A bidiyon, an ganshi tare da su Aliko Dangote, Sanata Barau da kuma Ahmad Lawal, tsohon shugaban majalisa

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Aso Rock Villa, Abuja - Umar Bush, wani dan Arewa da ya yi shuhura wajen dura ashariya ga aboki tafiyarsa ya samu damar shiga fadar shugaban kasa a wata gayyata.

Kara karanta wannan

Fashin magarkama: 'Yan Boko Haram sama da 100 sun tsere daga gidan yarin Nijar

Wani bidiyo ya nuna lokacin da Bush da ‘yan tawagarsa ke cikin Villa, inda ya gamu da wasu fitattun ‘yan Najeriya.

Yadda Umar Bush ya gamu da su Dangote a Villa
Umar Bush ya gamu da su Dangote a Villa | Hoto:@offcial_umar_bush
Asali: TikTok

Waye Umar Bush?

Bush dai wani fusataccen mutum da ake fargabar yana da tabin hankali, inda ake ganinsa a bidiyo a kafafen sada zumunta ya banka ashariya ga abokin tafiyarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokuta daban-daban, yakan dura ashariyar ne a salo na fushi da nuna an bata masa rai kan abin da bai taka kara ya karya ba.

Wannan yanayi na fusata da bacin rai ya sa ya yi suna ainun, har ta gai yake haduwa da manyan mutanen Najeriya da sunan barkwanci.

Bush ya gamu da su Dangote

A bidiyon da ya yadu kwanan nan, an ga lokacin da Bush ke tare da ‘yan tawagarsa a Villa, inda suke tare da su Aliko Dangote da Sanata Barau har da tsohon shugaban majalisa Ahmad Lawal.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, gwamnati ta dauki matakin gaggawa domin samar da abinci

A takaitaccen bidiyon, alamu sun nuna an yi wani taro a Villa, har ta kai ga aka gayyaci Umar Bush da abokansa.

Jama’ar kafar sada zumunta sun bayyana mamakin tashin Umar Bush daga mutumin da ba komai ba zuwa fitacce.

Kalli bidiyon:

Yadda Hisbah ta zauna da Umar Bush

A baya kun ji cewa, hukumar Hisbah mai kokarin dabbaka shari’ar musulunci a jihar Kano ta yi magana a game da Umar Bush da ya yi suna a yau.

Umar Bush wani mutumi ne da ya samu daukaka musamman a ‘yan kwanakin bayan nan saboda yadda ya ke dirka ruwan ashar.

Shugaban dakarun Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya koka game da yadda ake tunzura wannan bawan Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.