Yau ake gudanar da jana'izar tsohon shugaban amurka HW Bush

Yau ake gudanar da jana'izar tsohon shugaban amurka HW Bush

- A ranar Larabar nan, 05 ga watan Disamba, 2018, hudu daga cikin tsoffin shuwagabannin kasar Amurka tare da shugaba mai ci a yanzu, suka hallarci jana'izar George HWalker Bush

- A ranar Juma'a, 30, ga watan Nuwambar 2018 ne tsohon shugaban kasar HW Bush ya mutu yana da shekaru 94 a duniya, haka zalika shine shugaban kasar Amurka na 41

- Daga cikin shuwagabannin da zasu halarci jana'izar, akwai Yarima Charles na kasar Burtaniya; shugabar Jamus Angela Merkel, da Lech Walesa, tsohon shugaban kasar Poland

A ranar Larabar nan, 05 ga watan Disamba, 2018, hudu daga cikin tsoffin shuwagabannin kasar Amurka tare da shugaba mai ci a yanzu, Mr Donald Trump, suka hallara domin ganawar karshe da tsohon shugaban kasar George Herbert Walker Bush.

A ranar Juma'a, 30, ga watan Nuwambar 2018 ne tsohon shugaban kasar HW Bush ya mutu yana da shekaru 94 a duniya, haka zalika shine shugaban kasar Amurka na 41.

Daga cikin tsoffin shuwagabannin Amurkan guda hudu da zasuyiwa HW Bush bankwana a yau, sun hada da Jimmy Carter, Bill Clinton, Barak Obama inda zasu hadu da Shugaba Donald Trump, don nuna alhininsu ga HW Buhs, a babbar cocin kasa dake birnin Washington DC.

KARANTA WANNAN: Zan kawo karshen Boko Haram ta hanyar diflomasiyya - Atiku Abubakar

Yau ake gudanar da jana'izar tsohon shugaban amurka HW Bush
Yau ake gudanar da jana'izar tsohon shugaban amurka HW Bush
Asali: Depositphotos

Haka zalika, akwai wadanda zasu gabatar da jawabi a wajen wannan ganawar bankwanar, da suka hada da, tsohon Firai Minista Brain Mulroney na kasar Canada, tshohon Sanatan Amurka Alan Simpson, sai kuma shaharraren masanin tarihi Jon Meacham, tare da babban marubucin tarihin mamacin shugaba Bush babba.

Daga cikin shuwagabannin kasashen duniya da zasu halarci jana'izar, akwai Yarima Charles na kasar Burtaniya; shugabar Jamus Angela Merkel, da Lech Walesa, tsohon shugaban kasar Polnad.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng