Rijiyar Kolmani: Gwamnan Arewa ya Gana da Tinubu kan Batun Hako Mai a Arewa

Rijiyar Kolmani: Gwamnan Arewa ya Gana da Tinubu kan Batun Hako Mai a Arewa

  • A lokacin da ake zargin wasu jiga-jigan gwamnati na hana sauran jami'ai ganawa da Tinubu, gwamnan Gombe ya samu ganin shugaban
  • Gwamnan Inuwa Yahaya ya gana da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a kan batutuwa da dama ciki har da rijiyar man Kolmani
  • Tun bayan kaddamar da gagarumin aikin da ya dauki hankali shekaru biyu baya, ba a sake jin duriyar ci gaba da aiki a wurin ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Ana tsaka da cece-kuce kan cewa mukarraban gwamnati ba sa iya ganawa da shugaban kasa, Bola Tinubu, gwamnan jihar Gombe Inuwa Yahaya ya samu ganinsa. A ganawar, an tattauna batutuwa da dama ciki har da batun rijiyar man Arewa ta Kolmani da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata, NLC ta dage kan N250,000

Gombe
Gwamnan Gombe ya gana da Tinubu kan batutuwan rijiyar man Kolmani, abinci Hoto: Ismaila Uba Misilli
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, daraktan yada labarai na gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Uba Misilli ya ce gwamna Inuwa ya nuna takaicin rashin ci gaba a aikin a mahakar.

Gwamna ya yi takaicin kin hakar fetur

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayyana takaici kan yadda aka watsar da lamarin rijiyar hakar man Kolmani shekaru biyu bayan kaddamar da ita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Nation ta wallafa cewa aikin filin hakar danyen mai na Kolmani ya hada da matatar fetur mai karfin aikin 250,000, da wurin samar da takin zamani.

Ya ce amma duk da moriyar da za a samu, kamfanin mai na kasa NNPCL ya yi watsi da aikin, inda ya yi zargin ko matsala aka samu.

Kila a dawo da aiki a Kolmani

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce tunda batun man fetur ba ya karkashinsu, babu wani abu da za su iya yi a kan mahakar man Kolmani.

Kara karanta wannan

Ana murnar samun 'yancin kananan hukumomi, ciyaman ya nada hadimai 100

Amma ya na ganin tunda sun tattauna a kan lamarin da shugaban kasa Muhammadu Buhari, akwai yiwuwar a dawo da aiki a mahakar.

Shugaba Buhari ya kaddamar da mahakar mai

A baya mun ruwaito cewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da mahakar danyen mai a Arewa.

Mahakar man Kolmani da aka kaddamar a jihar Gombe ita ta ce ta farko a yankin, kuma tuni samfurin danyen mai ya fito daga mahakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.