A Karshe: Tinubu Ya Yarda Akwai Yunwa a Najeriya, Ya Dauki Sabon Mataki
- Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa yunwa ta yi katutu ga al'ummar Najeriya saboda matsaloli mabanbanta
- Biyo bayan haka, gwamantin ta kafa sabon kwamitin yaki da yunwa da zai tabbatar da abinci ya wadata a Najeriya
- Mambobin kwamitin sun fara bayyana matakin da za su dauka domin ganin an yaki yunwa da samar da abinci a fadin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana dauki matakin gaggawa bayan amincewa akwai yunwa a Najeriya.
A yau juma'a, 12 ga watan Yuli mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya kaddamar da kwamitin a fadar shugaban kasa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin ta tattatauna da wasu gwamnonin jihohi da masana kan yadda za a samu mafita.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shettima: 'Akwai yunwa a Najeriya'
Mataimakin shugaban kasa ya tabbatar da cewa a yanzu ba za a cigaba da musu kan cewa akwai yunwa a Najeriya ko babu ba.
Kashim Shettima ya ce dole ne a yarda cewa Najeriya na fama da matsalar abinci domin a fara neman mafita.
Aikin kwamitin yaki da yunwa
Yayin da yake jawabi, Sanata Kashim Shettima ya ce ba a kafa kwamitin domin ya zama kishiya ga ma'aikatar noma ba.
Ya ce kwamitin zai yi aikin gaggawa ne domin ganin an magance matsalolin abinci kawai a Najeriya, rahoton the Guardian.
Yan kwamiti sun bayar da shawara
Gwamnonin da ke cikin kwamitin sun tabbatarwa gwamnati cewa akwai bukatar sake duba yadda ake noma a Najeriya.
Gwamna Babagana Umara Zulum ya ce an kara yawa sosai a Najeriya kuma ba a noman da za ta ciyar da mutane saboda haka ya kamata a shigo da tsarin zamani a harkar noma.
Za a bunkasa noma a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta dauki sabon mataki kan bunkasa harkokin noma domin samar da wadataccen abinci a fadin Najeriya.
A sabon yunkurin, gwamantin shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu za ta samar da motocin noma da dama da wasu kayayyaki.
Asali: Legit.ng