Gida Bai Koshi ba: An Damke Ganguna 85 na Fetur za a yi Safararsu Zuwa Ketare
- Yayin da jama'a a kasar nan ke kukan rashin man fetur da tsadarsa, an gano wasu masu kokarin safarar man zuwa Kamaru
- Hukumar kwatsam shiyyar Adamawa/Taraba ce ta damke ganguna da jarkoki makare da fetur din a iyakar kasar nan
- Shugaban hukumar a shiyyar, Garba Bashir ya ce sun samu nasarar kama wasu kayan da kudinsu ya kai N36.9m
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Adamawa - A lokacin da 'yan Najeriya ke fama da dawowar layukan mai, hukumar kwastam ta cafke wasu dauke da fetur da za a yi safararsa zuwa kasar waje.
Jami'an hukumar kwastam da ke kula da shiyyar Adamawa/Taraba ne su ka cafke wadanda ake zargi da safarar fetur din.
Jaridar The Nation ta wallafa cewa an kama mota da ganguna 85 dauke da lita 200 kowanne na fetur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An kama jarkokin fetur a iyakar Kamaru
Hukumar kwastam ta bayyana kama jarkoki lita 25 dauke daga 795 na fetur zuwa kasar Kamaru. Shugaban hukumar shiyyar Adamawa/Taraba , Garba Bashir ne ya bayyana haka ga manema labarai a babban ofishinsu da ke Yola a yau Juma'a.
Naira land ta wallafa cewa an kama mota kirar Carina E da wani boyayyen sashi da aka killace jarkokin dauke da fetur.
An kama kayan N36.9m cikin mako shida
Shugaban hukumar kwastam shiyyar Adamawa/Taraba, Garba Bashir ya kara da cewa sun yi kamen harkokin man fetur din ne daga 29 Yuni, 2024 zuwa yanzu.
Ya ce a cikin mako shida, sun yi kame sau 17 na abubuwan da aka hana tsallaka wa da su waje, kuma kudinsu ya tasamma N36.9m.
kwatsam ta gano dalilin karancin fetur
A baya mun kawo labarin cewa hukumar kwatsam ta kasa ta bayyana dalilin da ya sa ake fuskantar karancin mai a wasu sassan kasar nan.
Shugaban hukumar, Bashir Adewale Adeniyi ya ce sun kai samame iyakokin kasar nan inda su ka yi nasarar cafke fetur da aka yi niyyar fita da su.
Asali: Legit.ng