Kanjamau: Ma’aikatar Lafiya ta Gano Dalilin Yawaitar Mutuwar Jarirai a Najeriya

Kanjamau: Ma’aikatar Lafiya ta Gano Dalilin Yawaitar Mutuwar Jarirai a Najeriya

  • Gwamnatin tarayya ta koka kan cigaba da yawaitar mutuwar yara kanana saboda cuta mai karya garkuwar jiki a Najeriya
  • Bayan yawaitar mutuwar, ma'aikatar lafiya ta bayyana cewa ana cigaba da samun karin yara da suke kamuwa da muguwar cutar
  • Ƙaramin ministan lafiya na kasa, Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana takaici kan lamarin a jiya Alhamis yayin wani taro a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta koka kan yadda cutar kanjamau ke jawo mace macen yara a Najeriya.

Haka zalika gwamnatin ta nuna takaici kan yadda iyaye mata ke yada cutar kanjamau ga yaransu.

Kanjamau
An bayyana yadda kanjamau ke kashe yara a Najeriya. Hoto: Stefan Heunis
Asali: Getty Images

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa karamin ministan lafiya, Dakta Tunji Alausa ya bayyana adadin yaran da cutar ta hallaka a Najeriya.

Kara karanta wannan

'Ana shan wuya,' Wani babba a APC ya cire kunya ya koka kan mulkin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin yara masu kanjamau a Najeriya

Karamin ministan lafiya, Dakta Tunji Alausa ya tabbatar da cewa akwai yara kimanin 140,000 masu ɗauke da cutar kanjamau a Najeriya.

Bayan haka, Dakta Tunji Alausa ya bayyana cewa Najeriya tana samun yara kimanin 22,000 masu kamuwa da cutar duk shekara.

Ya kuma tabbatar wa manema labarai cewa yawanci yaran na kamuwa da cutar ne ta hanyar iyayensu.

Yaran da kanjamau ta kashe a Najeriya

Haka zalika ministan lafiyar ya bayyana cewa cutar kanjamau tana kashe yara akalla 15,000 duk shekara a Najeriya.

Dakta Tunji ya ce kididdiga ta nuna cewa a duk mako kimanin yara masu kanjamau 300 ne ke mutuwa, rahoton the Guardian.

Kanjamau ta gagara karewa a Najeriya

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa a kokarin rage cutar kanjamau da ake an yi nasara ne kawai da kashi 35% alhali kasashen duniya sun samu nasara da kashi 95%.

Kara karanta wannan

An canza salo: Gwamnatin Najeriya ta fitar da bayanai kan yi wa yan bindiga tarko

Saboda haka ne gwamnati ta ce dole a kara daukan mataki da za a magance matsalar domin samun nasara kan yaki da cutar.

An samo maganin kanjamau

A wani rahoton, kun ji cewa gamayyar wasu masana kimiyya sun samar da hanyar magance cutar kanjamau a kasar Amurka.

Rahoton da kafafen yada labarai na waje suka fitar ya bayyana cewa, an samu matar da ta warke sarai daga kanjamau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng