Mafi yawancin direbobin manyan motocci na dauke da kwayar cutar kanjamau - NACA

Mafi yawancin direbobin manyan motocci na dauke da kwayar cutar kanjamau - NACA

- Direbobin manyan motocci suna daga cikin wanda suke kan gaba wajen yadda cutar HIV/AIDS

- Mafi yawan direbobin suna jima'i da wasu matan a lokacin da su kayi nisa da gida ba tare da wata kariya ba

- Hakan yasa NACA ta fara shiri na musamman don wayar da kan direbobin

Hukumar kare yaduwar cutar kanjama na kasa (NACA) ta bayyana cewa mafi yawan masu dauke da cutar nan ta Kanjamau wato HIV/AIDs sun kasance direbobin manyan motocci ne.

Darakta Janar na NACA Dr Sani Aliyu ne ya bayyana haka a wani hira da suka gudanar a ranar Juma'a da jaridar Punch.

Aliyu yace binciken ya tabbatar da cewa mafi yawan direbobin manyan motoci suna saduwa da matan da ba nasu ba a lokacin da su kayi nisa da gida. Sannan su dawo gida su yada cutar ga matansu.

Mafi yawancin direbobin manyan motocci na dauke da kwayar cutar kanjamau - NACA
Mafi yawancin direbobin manyan motocci na dauke da kwayar cutar kanjamau - NACA

KU KARANTA: An kama wasu matasa biyu da laifin yiwa wata 'yar shekaru 14 fyade

Direkta Janar din na NACA yace wannan ne yasa hukumar ta bullo da wani sabon shirri don wayar da kan direbobin motoccin kan hadarin da janyo wa kansu da iyalansu wadda akayi wa lakabi da STOP: Strategic Travellers' Outreach Programme.

Yace "binciken ya nuna cewa direbobin manyan motocin basa amfani da kwaroron roba yayin da kashi 70% daga cikin su sun gogawa abokanan harkar su biyu zuwa biyar a cikin shekara daya wannan ya janyo yaduwar cutar cikin gaggawa".

Binciken shi zai kara bamu haske akan lamarin.

Daraktan na shirin na HIV\AIDS Dr Erasmus Morah yace akwai bukatar ma'aikatan tsaro don kawo karshen matsalar.

Ya kuma ce tunda ya tabata cewa mazajen a waje suka samo kwayar cutar, yana da muhimmanci gwamnati ta nemi hadin kan masu sayar da soyayar ba wai wulkanta su ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164