Zargin N33bn: Bayan Kwana 1 a Kurkuku, Kotu Ta Ɗauki Mataki Kan Ministan Buhari

Zargin N33bn: Bayan Kwana 1 a Kurkuku, Kotu Ta Ɗauki Mataki Kan Ministan Buhari

  • Kotu ta bayar da belin tsohon ministan wuta a gwamnatin Muhammadu Buhari a kan Naira Biliyan 10
  • Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ce ta shigar da kara kotu ta na tuhumar tsohon ministan da zambar N33bn
  • A ranar Alhamis kotu ta tura Saleh Mamman gidan kaso inda ya kwana gabanin sauraron bukatarsa ta neman beli

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Bayan kwana guda da tesa keyarsa gidan kurkuku bisa zargin badakalar N33bn, kotu ta bawa tsohon ministan wuta, Mamman Saleh ya damar biyan beli. A zamanta na ranar Juma'a, kotun tarayya karkashin Mai Shari'a James Omotosho ta bayar da belin tsohon ministan bisa wasu sharudda.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: 'Yan sanda sun yi ram da iyayen da suka saka ɗansu a kasuwa

Mamman Saleh
An bayar da belin tsohon ministan wuta a kan N10bn Hoto: Engr. Sale Mamman
Asali: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Mai Shari'a Omotosho ya bayar da belin a kan N10bn da kuma kawo mutane biyu da za su iya tsaya masa.

Kotu ta gindaya sharuddan beli

Mai Shari'a James Omotosho ya gindaya sharuddan da mutum biyu da za su tsayawa tsohon minista Mamman Saleh za su cika kafin a ba shi beli.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin sharuddan dole ne sai mutane biyun sun mallaki dukiya a babban birnin tarayya Abuja da kudinsu ya kai N750m. Sannan ana bukar takardar harajinsu na shekaru uku, takardar bayanan bankinsu da hotunan fasfo, Jaridar Blueprint ta wallafa Sauran sharadin da Mai Shari'a Omotosho ya gindaya shi ne dole sai Mamman Saleh ya bayar da fasfo dinsa.

N33bn: EFCC na zargin Mamman da badakala

Hukumar hana yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) na tuhumar Mamman Saleh da zambar N33bn lokacin ya na minista.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari zai kwana a gidan yarin Kuje, kotu ta yi hukuncin kan zambar N33.8bn

Ana tsaka da shari'ar zambar a jiya ne Mamman Saleh ya yanke jiki ya fadi, amma daga bisani aka aika da shi gidan kurkuku.

Tsohon ministan Buhari zai kwana a kurkuku

A wani labarin kun ji cewa tsohon ministan wuta a gwamnatin Muhammadu Buhari, Mamman Saleh ya fuskanci fushin kotu.

Mai Shari'a James Omotosho ne ya yanke hukuncin tura Mamman Saleh kurkuku har sai an duba bukatarsa ta samun beli.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.