Ana Shirin Zanga Zanga, Gwamnati ta Dauki Matakin Gaggawa Domin Samar da Abinci

Ana Shirin Zanga Zanga, Gwamnati ta Dauki Matakin Gaggawa Domin Samar da Abinci

  • Gwamnatin tarayya ta dauki sabon mataki kan bunkasa harkokin noma domin samar da wadataccen abinci a fadin Najeriya
  • A sabon yunkurin, gwamantin shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu za ta samar da motocin noma da dama da wasu kayayyaki
  • Matakin na zuwa ne a yayin da ake jin kishin kishin din cewa al'ummar Najeriya za su yi zanga zanga saboda yawaitar yunwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da daukan sabon mataki domin ganin abinci ya wadata a Najeriya.

Wannan matakin na zuwa ne bayan gwamnatin ta yi alkawarin cewa farashin abinci zai karye a cikin watanni masu zuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya mayar da martani bayan harbin Donald Trump, ya yi gargadi

Motar noma
Za a samar da motocin noma a Najeriya. Hoto: South_agency
Asali: Getty Images

Legit ta tatttaro bayanan ne cikin wani sako da mai taimakawa shugaba Bola Tinubu a kan harkokin sadarwa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai saye motocin noma

Bayo Onanuga ya wallafa cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da sayen motocin noma kirar tarakta kanana guda 2,000.

Mai taimakawa shugaban kasar ya kara da cewa shugaba Bola Tinubu ya kara bayar da umurnin sayen manyan tarakta guda 1,200.

Karin kayan noma da za a saye

Har ila yau, gwamantin tarayya ta kara da cewa za a saye garma da za a rika amfani da su samfura daban-daban.

A dunkule, za a saye garma kimanin 5,000 domin ganin ayyukan noma sun bunkasa a Najeriya, rahoton Leadership.

Kamfanin da za a ba kwangila

Bayo Onanuga ya bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ba da kwangilar aikin ne ga kamfanin harkar noma na MAP.

Kara karanta wannan

A karshe: Tinubu ya yarda akwai yunwa a Najeriya, ya dauki sabon mataki

A cewar Onanuga, kamfanin MAP ya jagoranci irin ayyukan a ƙasashen Zimbabwe, Kenya, Togo da South Africa.

Gwamnati ta dauke haraji

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta fara daukar matakin sauko da farashin kayan abinci da su ka yi tashin gwauron zabo a daukacin kasuwannin kasar nan.

Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari ya ce an dakatar da harajin wasu nau'in abinci domin saukakawa yan kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng