Aikin noma: Manoman alkama sun koka a kan gwamnati ta yi watsi da su

Aikin noma: Manoman alkama sun koka a kan gwamnati ta yi watsi da su

- Kungiyar manoman alkama ta koka a kan gwamnati ta yi watsi da mambobinta

- Shugaban kungiyar ya ce ma'aikatar aikin gona ta tarayya ta manta da su tun lokacin da Cif Audu Ogbeh ya zama minista

- Shugaban ya ce a bara sun yi noman alkama kusan tons dubu dari shida a fadin kasar

Kungiyar manoman alkama a Najeriya wato ‘Wheat Farmers Association of Nigeria (WFAN)’sun yi zargin cewa ma'aikatar aikin gona ta tarayya ta manta da su tun lokacin da Cif Audu Ogbeh ya zama ministan ayyukan gona.

Legit.ng ta tattaro cewa, shugaban kungiyar, Alhaji Salim Muhammad, ya yi wannan zargin a lokacin da yake zantawa da manema labarai game da halin da ake ciki a harakar noman alkama a kasar.

Ya ce yana da matukar damuwa cewa duk da shirin gwamnatin tarayya a kokarin inganta ayyukan noma a kasar, amma an bar manoman alkama su ci gashin kansu.

Aikin noma: Manoman alkama sun koka a kan gwamnati ta yi watsi da su

Alkama

"A bara, mun yi noman alkama kusan tons dubu dari shida a fadin kasar, amma abin takaici shine an bar manoman da kayansu saboda ba za su iya sayarwa a kan abin da ake tayawa a kasuwa ba, kuma wannan lamarin ta shafi noman alkama na bana da kuma dukkan alamomi, samarwa zai kasance kasa da na shekarar bara" , in ji shi.

KU KARANTA: Gwamna Tambuwal ya kaddamar da fara sayar da takin da aka sarrafa a jihar Sokoto

Ya kara da cewa, ko da yake ƙungiyar ta karu da yawan mambobi, manoman alkama a Jihar Kano ba su tafi gona a wannan kakar ba saboda gaskiyar abincin su na bara har yanzu ba shi da kyau.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel