Kotun Koli Ta Ba Gwamnoni Sabon Umarni Kan Shugabannin Kananan Hukumomi a Najeriya

Kotun Koli Ta Ba Gwamnoni Sabon Umarni Kan Shugabannin Kananan Hukumomi a Najeriya

  • Kotun Ƙoli na ci gaba da yanke hukunci a ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar da gwamnoni 36 na ƙasar nan kan ƙananan hukumomi
  • Kotun Ƙolin ta hana gwamnoni 36 na ƙasar nan tsige zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi daga muƙamansu, inda ta ce hakan ya saɓawa doka
  • Tun da farko a ƙara, kotun ta yi hukuncin cewa gwamnatin tarayya ta riƙa ba ƙananan hukumomi kuɗaɗensu kai tsaye ba ta hannun gwamnoni ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kotun Ƙoli ta hana gwamnoni tsige zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomi a ƙasar nan.

A hukuncin da Kotun Ƙolin ta yanke a ranar Alhamis, ta ce yin hakan ya saɓawa kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta shirya yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar d agwamnoni

Kotun Koli ta ba gwamnoni umarni
Kotun Koli ta hana gwamnoni cire ciyamomi Hoto: @WATLegal
Asali: UGC

Kotun kolin ta ce waɗanda ake ƙara (gwamnoni) kawai sun ɓata lokacinsu ne a ƙarar, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin tarayya ce dai ta shigar da ƙarar a gaban kotun domin nemawa ƙananan hukumomin ƴancin cin gashin kansu.

Kotun Ƙoli ta zartar da hukuncinta

Kotun Ƙolin ta kuma ba da damar ƴancin gashin kai kan harkokin kuɗi ga ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.

A hukuncin da mai shari’a Emmanuel Agim ya karanta, Kotun Ƙolin ta caccaki gwamnonin kan hana ƴancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi na tsawon shekaru da dama.

Mai shari’a Agim ya bayyana cewa ya kamata ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan su riƙa tafiyar da harkokin kuɗaɗensu da kansu.

Kotun Ƙolin ta bayar da umarnin cewa daga yanzu a riƙa biyan kuɗaɗen ƙananan hukumomi zuwa asusunsu kai tsaye daga asusun tarayya, ba a asusun gwamnatin jihohi ba kamar yadda ake yi a baya.

Kara karanta wannan

PDP ta dauki mataki bayan kotu ta soke zaben fidda gwaninta na gwamna

Kotun Ƙoli ta shirya yanke hukunci

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kotun ƙoli ta shirya yanke hukunci kan ƙarar da gwamnatin tarayya ta shigar da gwamonin 36 na ƙasar nan.

Gwamnatin tarayya ta shigar da ƙarar ne domin neman cikakken ƴancin cin gashin kai ga ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng