Gwamnoni Na Kukan Rashin Kudi, Za a Gina Tashar Motar Biliyoyin Naira a Zamfara
- Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da kashe Naira Biliyan 4.8 domin gina tashar mota irinta ta farko a Gusau
- Za a sanya gine-ginen zamani da su ka hada da tashar kashe gobara, ofishin 'yan sanda da dakin adana kayayyaki
- Gwamnatin jihar ta bakin mai magana da yawun gwamna Dauda Lawal, Sulaiman Bala Idris ta tabbatar da batun
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Zamfara- Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da fitar da Biliyoyin Naira domin gina tashar motar zamani a Gusau. Majalisar zartarwar jihar ta amince a fitar da N4,854,135,954.53 domin samar da tashar mota irinta ta farko a Zamfara.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris ya ce za a bayar da kwangilar gina tashar ga Fieldmark Construction Ltd.
Me za a samar a tashar N4.8bn?
Jaridar Punch ta tattaro cewa za a gina kasaitacciyar tashar Biliyoyin Naira ne a yunkurin gwamnati na zamanantar da babban birnin jihar Zamfara, Gusau.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a samar da ofisoshin amfanin gwamnati da kungiyoyin masu ababen hawa, tashar kashe gobara da gidan baƙi.
Sauran abubuwan da za a sanya a cikin tashar sun hada da asibiti, ofishin 'yan sanda, wurin POS, gidan adana kayayyaki da wurin gyaran motoci.
Katafaren aikin na zuwa a gabar da gwamnonin Najeriya ke cewa ba za su iya biyan mafi karancin albashi ba matukar ya kai N62,000.
Ana gina filin jirgin sama a Zamfara
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da aikin gina filin jirgin sama a Zamfara, inda ake sa rai zai habaka tattalin arzikin jihar.
A jawabinsa, ministan harkokin sufuri, Festus Keyamo ya bayyana cewa jihar Zamfara na baya-baya a batun manyan ayyukan raya kasa.
Gwamna Dauda Lawal na jihar na ganin samar da filin jirgin saman zai haɓaka kasuwancinsu da bunƙasa harkar noma da aka sansu da shi.
Asali: Legit.ng