An Shiga Jimami Bayan Sanata Na'Allah Ya Tafka Babban Rashi, Buhari Ya Kaɗu

An Shiga Jimami Bayan Sanata Na'Allah Ya Tafka Babban Rashi, Buhari Ya Kaɗu

  • Sanata Bala Ibn Na'Allah ya tafka babban rashi bayan sanar da rasuwar matarsa mai suna Safiya Na'Allah
  • Matar sanatan da ya wakilci mazabar Kebbi ta Kudu ta rasu ne da yammacin jiya Talata 9 ga watan Yulin 2024
  • Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon ta'aziyya ga sanatan inda ya ce tabbas an tafka babban rashi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon ta'aziyya ga Sanata Bala Ibn Na'Allah.

Buhari ya tura sakon ne domin jajanta masa bayan rasuwar matar sanatan mai suna Safiya Na'Allah.

Buhari ya jajantawa Sanata Na'Allah kan rashin da ya yi
Muhammad Buhari ya tura sakon ta'aziyya ga Sanata Bala Na'Allah kan rasuwar matarsa. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Buhari ya tura sakon ta'aziyya ga Na'Allah

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura sakon jinjina ga Sheikh Dahiru Bauchi bayan cika shekaru 100

Mai magana da yawun Buhari, Garba Shehu shi ya bayyana haka a shafinsa na X a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Garba Shehu ya ce Buhari ya kira sanatan musamman a waya domin jajanta masa inda ya ce tabbas ya tafka babban rashi.

Tsohon shugaban ya ce iyalan sun yi rashin mutumiyar kirki inda ya ce sanatan ya yi rashin abokiyar zama.

"Marigayiyar Safiya ta cika duk wata mata da miji zai mallaka, rashinta babban gibi ne wanda zai yi wahalar cikewa."

- Muhammadu Buhari

Daga karshe, Buhari ya yi addu'ar ubangiji ya yi mata rahama da gafarta mata dukan zunubanta.

Mukamin da Sanata Na'Allah ya rike a Majalisa

Marigayiyar Safiya Na'Allah ta rasu ne da yammacin jiya Talata 9 ga watan Yulin 2024.

Sanata Na'Allah ya wakilci mazabar Kebbi ta Kudu a Majalisar Dattawa ta takwas da ke Abuja.

Kara karanta wannan

"Tuna halacci ke hana ni ɗaukar wasu matakai": Gwamna ga mai gidansa

Na'Allah ya rike mukamin mataimakin shugaban masu rinjaye a Majalisar ta takwas.

Buhari ya jajantawa Ministar Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajantawa Ministar harkokin ƴan sanda, Imaan Sulaiman-Ibrahim.

Buhari ya tura sakon ta'aziyya ga Ministar bayan rasuwar mahaifinta mai suna Hajiya A'isha a birnin Lafia da ke jihar Nassarawa.

Tsohon shugaban kasar ya ce tabbas rasuwar marigayiyar babban rashi ne inda ya bukaci iyalanta da su suyi koyi da kyawawan halayenta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.