Bayan Matakin Bude Iyakokin Kasa, Gwamnati Ta Fadi Lokacin Ragargajewar Farashin Abinci
- Gwamnatin tarayya ta yi albishir ga jama'ar kasar nan kan karyewar farashin abinci bayan koke da 'yan Najeriya ke yi na tsada
- Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ya bayyana cewa nan da kwanaki 180 farashin abinci zai yi warwas a kasuwannin Najeriya
- Matakin na zuwa kwanaki kadan bayan gwamnatin ta bayyana cewa za a bude iyakokin kasar nan domin shigo da abinci, tare da janye harajin shinkafa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Abuja - Yayin da 'yan Najeriya ke kukan yunwa, ministan noma da samar da abinci, Abubakar kyari ya bayyana ranar karyewar farashin abinci.
Wannan na zuwa ne bayan majalisar kasar nan ta gargadi gwamnatin tarayya kan cewa hakurin 'yan Najeriya ya kusa karewa saboda yunwa da fatara.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, minista Kyari ya bayyana cewa an dauki matakan da za su karya farashin abinci cikin kwanaki 180.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun dauki matakin karya farashi," Minista
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ta fara daukar matakan da za su karya farashin abinci domin saukakawa talakawa.
Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari ne ya bayyana haka, inda ya ce nan gaba kadan za a fara ganin sakamakon matakan.
“ Gwamnatinmu ta samar da wasu jerin matakai da za su magance matsalar hauhawar farashin abinci da ke addabar kasar nan. Za a aiwatar da wadannan matakai cikin kwanaki 180.
- Abubakar Kyari
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa ko a baya, ministan ya bayyana cewa gwamnati za ta shigo da wasu kayan abinci kasar nan domin rage matsalar yunwa da karya farashin kayan abinci saboda tsadar da su ka yi.
Gwamnati za ta bawa manoma tallafin N3.5bn
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Jigawa ta ware N3.5bn domin tallafawa manoma da niyyar habaka noman yankin a bana.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al'adu na jihar, Sagir Musa ne ya bayyana haka, kuma ya ce akalla manoma 30,000 za su amfana.
Asali: Legit.ng