Ana Fafutukar Bawa Mata Mukaman Gwamnati, An Gano Minista Ta Kashe Miliyoyi Kan Sayen Auduga

Ana Fafutukar Bawa Mata Mukaman Gwamnati, An Gano Minista Ta Kashe Miliyoyi Kan Sayen Auduga

  • Majalisar wakilan Najeriya ta yi zargin ministar mata Uju Kennedy Ohanenye da bushasha da kudin gwamnati kan abubuwan da ba su dace ba
  • Ana zargin Minista Uju da kashe miliyoyi domin gudanar da bikin sabuwar shekara da ma wasu Miliyan 1.5 kan sayen fetur
  • Kwamitin majalisar kan harkokin mata ta ce za a yi binciken ma'aikatar bayan 'yan kwangila sun yi korafin cewa an hana su kudinsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Majalisar wakilan Najeriya ta zargi ministar mata Uju Kennedy Ohanenye da almubazzarancin kudin gwamnati ta hanyoyin da ba su dace ba.

Wannan na zuwa a gabar da ake rajin samun karuwar mata a cikin harkar gudanar da gwamnatin kasar nan a matakan jihohi da tarayya.

Kara karanta wannan

Cikakkun sunaye da bayanan jihohi 7 da ake son kirkira a Najeriya

Uju Kennedy Ohanenye
Ana zargin ministar ma'aikatar mata da almubazzaranci Hoto: Uju Kennedy Ohanenye
Asali: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa kwamitin lura da ayyukan mata na majalisar wakilai karkashin jagorancin Kafilat Ogbara ya zargi minista Uju da kashe N45 million wajen bikin sabuwar shekara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An kashe N20m kan audugar al'ada," Majalisa

Kwamitin al'amuran mata ya bayyana damuwa kan yadda ministar mata, Uju Kennedy Ohanenye ta barnatar da kudin gwamnati.

Shugabar kwamitin, Kafilat Ogbara ta zargi Minista Uju da sayen audugar al'ada na N20 da kuma sayen man fetur a motoci na N1.5m.

Nigerian Tribune ta wallafa cewa an gano haka ne bayan 'yan kwangila sun koka kan yadda ma'aikatar mata ta hana su kudadensu duk da cewa sun kammala aiki.

Haka kuma kwamitin zai yi bincike kan kudin da aka ware da ya kai N1.5bn domin biyan bashin da 'yan kwangila ke bin ma'aikatar.

Mistar Mata ta goyi bayan auren marayu

Kara karanta wannan

N1.5b: Majalisa ta dakatar da ayyuka a ma'aikatar mata, ta bukaci minista ta gurfana

A baya kun ji cewa ministar mata, Uju Kennedy Ohanenye ta zubar da makamanta, inda ta goyi bayan aurar da marayu 100 a jihar Neja bayan ta tirje da fari.

Da farko dai ministar ta ki amincewa da auren marayun, amma daga baya ta basu kyaututtuka da suka hada da zannuwa da kayan karatu a matsayin gudunmawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.