Dan Majalisar Tarayya Ya Sake Mutuwa Watanni 2 Bayan Rasuwar Dogonyaro Daga Jigawa
- Majalisar Tarayya a Najeriya ta sake shiga jimami bayan rasuwar wani mambanta daga jihar Oyo a Kudancin kasar
- Marigayin mai suna Hon. Musiliu Olaide Akinremi ya kasance mamban Majalisar karo na biyu da ke wakiltar mazabar Ibadan ta Arewa
- Wani jigon jam'iyyar APC a jihar Oyo, Akin Akinwale shi ya tabbatar da rasuwar ɗan Majalisar a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Oyo - An shiga jimami bayan rasuwar ɗan Majalisar Tarayya daga jihar Oyo a Kudancin Najeriya.
Marigayin mai suna Musiliu Olaide Akinremi da ke wakiltar mazabar Ibadan ta Arewa ya rasu ne a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024.
Oyo: An shi rashin dan Majalisar Tarayya
Jigon jam'iyyar APC a jihar, Akin Akinwale shi ya bayyana haka a shafin X a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akinwale ya bayyana rasuwar ɗan Majalisar Tarayyar a matsayin abin takaici da bakin ciki.
"Mun yi babban rashin Hon. Musiliu Olaide Akinremi da ke wakiltar mazabar Ibadan ta Arewa a Majalisar Tarayya."
"Wannan babban rashi da aka yi abin takaici ne da bakin ciki. Allah sarki."
- Akin Akinwale
Rahotanni sun tabbatar da cewa an dauko gawar marigayin domin gudanar da sallar jana'izarsa a Ibadan da misalin karfe 4.00 na yamma.
Mene musabbabin mutuwar ɗan Majalisar a Oyo?
Sai dai har zuwa lokacin tattara wannan rahoto ba a bayyana musabbabin mutuwar marigayin ba.
Duk da haka wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC ciki har da Akinwale sun tabbatar da rasuwar marigayin a yau Laraba 10 ga watan Yulin 2024.
Marigayin da aka fi sani da 'Jagaban' yana wa'adinsa na biyu ne a Majalisar Wakilai ta Najeriya.
Wannan mutuwa na zuwa ne watanni biyu bayan rasuwar Isa Dogonyaro daga jihar Jigawa a Majalisar Wakilai.
Mahaifiyar Ministar masana'antu ta rasu
A wani labarin, kun ji cewa mahaifiyar Ministar kasuwanci da masana'antu, Doris Uzoka-Anite ta yi bankwana da duniya.
Marigayar mai suna Mrs Immaculata Uzoka ta rasu ne bayan ta sha fama da jinya mai tsayi kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Shugaba Bola Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiyar inda ya bukace su da su yi koyi da kyawawan halayenta.
Asali: Legit.ng