Sanata Ya Bayyana Abin da Yasa Tinubu Ya Gagara Shawo Kan Tsadar Abinci

Sanata Ya Bayyana Abin da Yasa Tinubu Ya Gagara Shawo Kan Tsadar Abinci

  • Sanata Ali Ndume daga jihar Barno ya bayyana manyan kalubalen da ke gaban gwamnatin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • Ali Ndume ya ce sun yi ƙoƙarin bayyanawa gwamantin yadda za a samu mafita amma ta kulle kofofin karbar shawara gam
  • Legit ta tattauna da Auwal Abba Koli domin jin yadda tsadar abinci take shafar rayuwar al'ummar yankin da yake

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sanata Ali Ndume ya gargadi gwamnatin tarayya kan daukar matakin da ya dace a kan tsada da wahalar abinci.

Sanatan ya ce akwai barazana babba ga Najeriya idan yanayin ya cigaba da tafiya a haka ba tare da samar da mafita ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya fadi sabon albashin da zai iya biyan ma'aikata, NLC ta dage kan N250,000

Ali Ndume
Ali Ndume ya yi magana kan tsadar abinci. Hoto: @Imranmuhdz
Asali: UGC

A cikin hirar da ya yi da BBC Hausa, Ali Ndume ya bayyana abin da ya kamata gwamnatin ta yi domin samar da mafita.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsadar abinci: Tinubu ya rufe kofa

Sanata Ali Ndume ya koka kan cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta rufe dukkan kofofin da za a rika fada mata gaskiya kan halin da ake ciki.

Ali Ndume ya bayyana cewa a cikin ministoci ma ba kowa ne ke samun ganin shugaban kasa ba balle su yan majalisu, rahoton Daily Trust.

Tsadar abinci: me ake tsoro ga Najeriya?

Ali Ndume ya nuna farga kan cewa idan yanayi ya cigaba da tafiya a haka watarana mutum zai nemi abinci da kudinsa ya rasa.

Ya ce a yanzu haka an fara shiga tsananin yunwa a jihar Katsina inda yara suka fara rasa abinci mai gina jiki kuma yanayin zai munana idan ba a dauki mataki ba.

Kara karanta wannan

Ana shirin zanga zanga, gwamnati ta dauki matakin gaggawa domin samar da abinci

Tsadar abinci: Me ya kamata Tinubu ya yi?

Ali Ndume ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta tara masana da yan kasa domin neman bahasi kan yadda za a magance matsalar.

Ya kuma kara da cewa dukkan wani mataki da gwamnatin za ta dauka ta rika sanar da jama'a domin hakan zai kwantar musu da hankali da rage musu radadi.

Legit ta tattauna da Auwal Koli

A cikin hirar da ya yi da Legit, Auwal Abba Koli ya bayyana cewa tsadar abinci ta yi mugun yawa a jihar Bauchi ta inda wasu al'umma ke kwana da yunwa.

Ya ce a halin yanzu yunwa ne ke kokarin tilasta mutane fita zanga zanga kuma ba a san ina abin zai tsaya ba.

Ali Ndume: 'Nijar za ta dawo Ecowas'

A wani rahoton, kun ji cewa dan majalisar wakilan kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta yamma, Sanata Ali Ndume ya ce kasashen da suka fita daga ECOWAS za su dawo.

Sanata Ali Ndume ya bayyana haka ne yayin hira da manema labarai bayan wani taron majalisar kungiyar da ya gudana a jihar Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng