Matsin Rayuwa: Sojojin Najeriya Sun Yi Aikin Jin Ƙai, Sun Raba Kayan Tallafi

Matsin Rayuwa: Sojojin Najeriya Sun Yi Aikin Jin Ƙai, Sun Raba Kayan Tallafi

  • Rundunar sojin Najeriya ta raba kayan tallafi ga wasu marasa karfi a jihar Filato domin saukaka musu rayuwa
  • Daga cikin waɗanda suka samu kayan tallafin akwai wani dalibin makarantar sakandare mai bukata ta musamman
  • Legit ta tattauna da wani farar hula, Isa Abubakar Hamma kan yadda yaji bayan karanta labarin abin da sojojin suka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Plateau - Rundunar sojin Najeriya ta raba kayan tallafi ga wasu mutane a jihar Filato ciki har da mai bukata ta musamman.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojin da ke karkashin rundunar Operation Safe Haven ne suka raba kayan tallafin.

Sojojin Najeriya
Sojoji sun raba tallafi a Filato. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Facebook

Legit ta tattaro bayanan ne a cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: 'Yan sanda sun yi ram da iyayen da suka saka ɗansu a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sojoji sun tallafi mai bukata ta musamman

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa ta hangi wani mai bukata ta musamman yana fama da tsohuwar keken hannu yayin zuwa makaranta.

Saboda haka ne sai ta yanke shawarar saya masa sabuwar keken hannu domin saukaka masa zuwa makaranta da sauran ayyuka.

Haka zalika rundunar ta umurce shi da ya rika zuwa asibitin sojoji domin ba shi kulawa ta musamman a ko da yaushe.

Sojoji sun raba tallafin keken dinki

A daya bangaren, rundunar sojin Najeriya ta raba tallafi keken dinki domin bayar da gudummawa wajen koyon sana'o'i.

An raba keken ɗinkin ne ga mutane uku kuma za su rika zuwa makarantar koyon sana'a ta kungiyar matan sojoji da ke Jos domin koyon dinki.

Rundunar ta ce hakan zai taimaka wajen rage zaman kashe wando da inganta tattalin arzikin waɗanda suka samu tallafin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun gwabza fada, hatsabibin mai garkuwa da mutane ya sheka lahira

Legit ta tattauna da Isa Abubakar

A hirar da Isa Abubakar Hamma ya yi da Legit ya bayyana cewa aikin tallafi da sojoji suka yi zai kara kusanto da su ga jama'a da kara musu taimako.

Isa Abubakar ya ce ya kamata sauran jami'an tsaro su yi koyi da abin da sojojin Najeriya suka yi wajen tallafawa al'umma.

Sojoji: 'Ba wariya a cikin aikinmu'

A wani rahoton, kun ji cewa Rundunar sojojin Najeriya ta musanta cewa ta na nuna wariyar addini ga jami'anta, inda ta ce babu gaskiya cikin labarin da ake yadawa.

Daraktan hulda da jama'a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka a matsayin martani ga masu zarginsu da wariya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng