"Hukumar NWDC Za Ta Warware Matsalolin Arewa Maso Yamma," Barau

"Hukumar NWDC Za Ta Warware Matsalolin Arewa Maso Yamma," Barau

  • Majalisar kasar nan na shirin mika kudirin kafa hukumar raya Arewa maso Yamma (NWDC) ga shugaban kasa Bola Tinubu
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, kuma wanda ya dabbaka kudurin Sanata Barau Jibrin ne ya bayyana haka a ranar Talata
  • Ya ce akwai kyakkyawan yakinin cewa shugaba Tinubu zai sanya hannu kan kudurin saboda muhimmancin da ya ke da shi ga ci gaban kasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja - Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Sanata Barau I. Jibrin ya ce akwai alamu mai karfi cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanya hannu kan kudirin kafa hukumar raya Arewa maso Yamma (NWDC). Ya bayyana haka ne bayan majalisun kasar nan sun amince da kudirin da a cewar Barau, ya zo dai-dai da ra'ayin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Gina layin dogo: Ana fama da matsin tattali, Tinubu zai karbo sabon bashi daga China

Barau
Majalisa za ta mika kudirin kafa hukumar NWDC ga shugaba Bola Tinubu Hoto: Barau I. Jibrin
Asali: Facebook

A sakon da mataimakin shugaban majalisar ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce an kammala shirin mika kudirin ga shugaban kasa domin ya sanya hannu.

"NWDC za ta kawo ci gaba," Barau

Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ce kafa hukumar raya Arewa maso Yamma zai kawo ci gaba mai dorewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta wallafa cewa Barau na ganin hukumar za ta warware matsalolin da su ke damun jihohin yankin guda bakwai da sauran sassan Najeriya.

Ya ce kasancewar Arewa maso Yamma ce rumbun abincin Najeriya, da zarar hukumar ta kafu za a fara gyara kayayyakin da rashin tsaro ya lalata a yankin.

"Kafa hukumar raya Arewa maso Yamma zai mayar da hankali wajen warware kalubalen da su ka addabi jihohin nahiyar ( (Kano, Kaduna, Katsina, Kebbi, Jigawa, Sokoto, da Zamfara) da ma kasa baki daya."

Kara karanta wannan

Tinubu zai sauka daga kujerar shugaban kungiyar ECOWAS yayin da wa'adinsa ya kare

- Barau I Jibrin

Jihohin Arewa maso Yamma sun nemi taimako

A wani labarin kun ji cewa gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma sun nemi agajin majalisar dinkin duniya kan matsalar tsaro a yankin.

Shugaban gwamnonin yankin kuma gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya ce akwai matsaloli da dama da yankin ke bukatar agaji a kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.