Jami’ar Bayero Ta Bayyana Dalilin Korar Dalibai 29 da Dakatar da Wasu
- Jami'ar Bayero da ke jihar Kano ta kori dalibai da dama daga makarantar bisa samunsu da aikata laifin da ya saɓa dokar jami'ar
- Haka zalika hukumar makarantar ta gargadi wasu dalibai da dakatar da wasu bisa samunsu da aikata laifuffuka daban daban
- Ana ganin matakin da jami'ar Bayero ta dauka yana cikin kokarin makarantar wajen samar da ingantacce da tsaftataccen ilimi a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Jami'ar Bayero (BUK) ta kori dalibai da dama bisa samunsu dumu-dumu da laifin satar amsa.
Har ila, yau makarantar ta dauki matakin ladabtarwa kan wasu daliban da aka samu da aikata laifi yayin jarrabawa.
Legit ta gano matakin da jami'ar ta dauka ne a cikin wani sako da makarantar ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalibai nawa aka kora a jami'ar Bayero?
Rahotanni sun nuna cewa jami'ar Bayero ta kori dalibai kimanin 29 bisa samunsu da laifin satar amsa.
Jami'ar ta ce bincike ya nuna cewa dukkan daliban sun aikata laifin satar amsa yayin rubuta jarrabawa.
jami'ar Bayero: An dakatar da dalibai
Hukumar gudanarwar jami'ar ta dauki matakin ladabtarwa a kan wasu dalibai guda uku sakamakon samunsu da laifi.
Jami'ar ta dakatar da guda biyu daga cikinsu tsawon rabin zangon karatu, daya kuma an dakatar da shi tsawon zangon karatu guda.
Jami'ar Bayero ta gargaɗi dalibai 15
Haka zalika jami'ar ta gardadi dalibai kimanin 15 bisa samunsu da rashin hali mai kyau yayin rubuta jarrabawa.
Hukumar makarantar ta bayyana cewa matakin da ta dauka na cikin kundin dokokin jami'ar, rahoton Leadership.
An kori dalibai a jami'ar Kwara
A wani rahoton, kun ji cewa akalla dalibai 175 ne aka kora daga jami'ar jihar Kwara (KWASU) da ke Malete, bayan an kamasu da aikata laifuffuka daban daban a makarantar.
Hukumar gudanarwar jami’ar ta ce laifuffukan sun hada da satar amsa, shiga haramtattun kungiyoyi, mallakar bindiga da sauran su.
Asali: Legit.ng