Gwamnan Yobe Ya Dakatar da Shugaban Karamar Hukuma, Ya Fadi Dalili

Gwamnan Yobe Ya Dakatar da Shugaban Karamar Hukuma, Ya Fadi Dalili

  • Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina a jihar daga kan muƙaminsa
  • Gwamna Mai Mala Buni ya ɗauki matakin dakatarwar ne bisa zargin rashin ɗa'a da rashin biyayya da ake yi kan Idrissa Mai Bukar Machina
  • A cikin sanarwar dakatarwar an buƙaci dakataccen shugaban da ya miƙa ragamar al'amuran ƙaramar hukumar ga mataimakinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina, Idrissa Mai Bukar Machina.

Gwamna Mai Mala Buni ya dakatar da shugaban ƙaramar hukumar ne bisa zargin rashin ɗa'a da rashin biyayya.

Gwamnan Yobe ya dakatar da shugaban karamar hukumar Machina
Gwamnan Mai Mala Buni ya dakatar da shugaban karamar hukumar Machina Hoto: Mai Mala Buni
Asali: Facebook

Gwamna Mai Mala Buni ya yi amfani da ikon da sashen na 2 na dokar ƙananan hukumomi ta shekarar 2019 wacce aka yiwa kwaskwarima ya ba shi wajen dakatar da shugaban ƙaramar hukumar, cewar rahoton jaridar Independent.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar NNPP ta bayyana matsayarta kan dakatar da Gwamna Abba da korar Kwankwaso

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran sakataren gwamnatin jihar, Shuaibu Abdullahi ya sanyawa hannu.

Meyasa Gwamna Buni ya dakatar da shugaban?

A cikin sanarwar, Gwamna Buni ya kuma umarci dakataccen shugaban ƙaramar hukumar da ya miƙa ragamar shugabancin ƙaramar hukumar a hannun mataimakinsa.

"Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, bisa ikon da sashe na 2 na dokar ƙananan hukumomi ta 2019 ya ba shi, ya amince da dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Machina, Idrissa Mai Bukar Machina, nan take saboda rashin ɗa’a da rashin biyayya."
"Bisa wannan dalilin, mai girma gwamna ya kuma umarci dakataccen shugaban ya miƙa al’amuran ƙaramar hukumar ga mataimakinsa har sai an ba da umarni na gaba."

- Shuaibu Abdullahi

Gwamnan Yobe ya naɗa sabon Sarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya naɗa babban ɗan marigayi Sarkin Tiƙau, Abubakar Muhammadu Ibn Grema a matsayin sabon sarkin masarautar.

Gwamna Mai Mala Buni ya naɗa sabon Sarkin Tikau ne biyo bayan rasuwar Mai Martaba Alhaji Muhammadu Abubakar Ibn Grema a cikin watan Mayun 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng