Kano: Mazauna Rano Na Cikin Tashin Hankali Kan Abubuwan da Ke Faruwa a Fadar Sarki

Kano: Mazauna Rano Na Cikin Tashin Hankali Kan Abubuwan da Ke Faruwa a Fadar Sarki

  • Mazauna garin Rano dake jihar Kano sun bayyana damuwarsu kan girke 'yan daba da makamai da aka yi a fadar sarki
  • An ruwaito cewa tun ranar Lahadi aka ga 'yan daban sun mamaye fadar, lamarin da ya dagawa jama'ar yankin hankali
  • A ranar Talata kuwa 'yan daban sun fito inda suke duka tare da harbin jama'a da danko, kamar yadda Legit Hausa ta tabbatar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Rano, Kano - Mazauna garin Rano da ke a jihar Kano, sun bayyana damuwarsu kan kawo 'yan daba da makamai da aka yi zuwa fadar masarautar a ranar Lahadi.

A wata wasika da aka aikawa kwamishinan 'yan sanda, an bayyana cewa an girke 'yan daban a fadar sarkin tun ranar Lahadin da ta gabata.

Kara karanta wannan

Auren jinsi: Yadda kururuwar mutanen Kano ya dakile yunkurin kungiyar LGBTQ

An girke 'yan daba a fadar Rano, jama'a suna adawa da wakilin sarkin Kano
Kano: Tura wakili fadar Rano ya jawo zanga-zanga. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Wasikar ta bayyana cewa har yanzu ba a san dalilin girke matasan da makamai ba, amma hakan na kokarin zama barazanar tsaro ta rayuka da kadarori, in ji rahoton The Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rano: An kai wa 'yan sanda koke

Wani bangare na wasikar koken da aka aikawa rundunar 'yan sandan Kano na cewa:

"A ranar Lahadi, 7 ga Yulin 2024, aka samu kutsen 'yan daba da makamai a garin Rano. Ana tsammanin wasu ne da ba a sani ba suka dauki nauyinsu kuma suka girke su a fadar sarki."

Kamar yadda wasikar ta bayyana, mazauna masarautar Rano mutane ne masu son zaman lafiya.

"A cikin shekarun nan, masarautar Rano ta fuskanci zaman lafiya mai dorewa, kuma jami'an tsaro za su iya tabbatar da hakan.
"Wannan rikicin masarautun na kwanan nan a jihar Kano, ya kawo tashin hankali da rashin natsuwa ga mazauna yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar NLC, an samu bayanai

'Yan daba sun far wa jama'a a Rano

A rahoton da Legit.ng ta tattaro daga Rano, ana zargin cewa 'yan daban sun bayyana ne domin bai wa wakilin Sarkin Kano, Mai martaba Muhammadu Sanusi II kariya.

A hirar da Legit.ng tayi da wani matashi mai suna Kamalu Baba, ya bayyana cewa, 'yan daban dai suna harbin jama'a da danko da gwafa.

Kamalu Baba ya ce lamarin ya faru a safiyar Talata bayan mazauna garin sun tirje sun ce basu bukatar wakilin da aka tura musu.

Wasu faifan bidiyo da Kamalu Baba ya turawa wakilinmu ya nuna lokacin da jama'a ke uhun 'bama so' yayin da suka mamaye wani titi na garin.

Sanusi ya tura wakili zuwa Nasarawa

A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa, ana tsaka da dambarwar sarautar Kano, Sarki Sanusi ya tura wakili Nasarawa.

Basaraken ya tura Abdullahi Sarki domin ya wakilcesa a karamar hukumar Nasarawa har zuwa lokacin da zai tura hakimin yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.