"Ya Yi Tasiri": Jarumar Fim Ta Fadi Yadda Kiran Salla Ke Burgeta, Ta Fara Son Musulunci
- Jarumar fim a masana'antar Nollywood, Tonto Dikeh ta yi magana kan yadda kiran salla ya yi tasiri a rayuwarta
- Dikeh ta ce sautin kiran salla ya sauya mata rayuwa inda ya kara kusanta ta da addini inda ta ce Musulmai suna burgeta
- Jarumar wacce Kirista ce ta ce tana neman shawara yadda za ta ba masallacin tallafi amma ba ta hanyar kudi ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Lagos - Jarumar fina-finan Nollywood, Tonto Dikeh ta yi magana kan yadda Musulmai ke burge ta.
Jarumar wacce Kirista ce ta ce yadda Musulmai ke rike addininsu hannu bibbiyu yana matukar burgeta.
Jaruma Tonto Dikeh ta magantu kan Musulunci
Tonto Dikeh ta bayyana haka ne a shafinta na Instagram inda ta ce tana jin dadin yadda ake kiran sallah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jarumar ta ce tana rayuwa kusa da masallaci wanda haka ya saka ta fara sha'awar Musulunci inda ta ce kullum tana tashi saboda kiran salla da ake yi.
Ta ce karar sautin kiran sallah yana kara kusanta ta ga Allah da kuma dagewa wurin yin addini.
Tonto Dikeh ta nemi shawara ƴan uwa
"Allah/Ubangiji abin so ne, gaskiya na sha jinin jikina, addu'ar da nake yi shi ne yadda zan fahimci Musulunci sosai."
"Yadda suke dagewa a wurin addininsu abin koyi ne, ina ji a jiki na kamar na je masallacin na tambaya me yasa basu yi sallah ba yau."
- Tonto Dikeh
Tonto Dikeh ta ce kiran salla ya yi matukar tasiri a rayuwarta inda ta bukaci shawara yadda za ta taimakawa masallacin ba ta hanyar kudi ba.
Jaruma ya soki Kiristoci kan Davido
A wani labarin, kun ji cewa jarumar fim a Najeriya, Merit Gold Eberechi ta soki Kiristoci kan taya Davido murnar aurensa.
Merit Gold ta ce bai kamata su taya shi murnar ba tun da sun sani ya haifi ƴaƴa har uku kafin aure wanda ya saba addini.
Jarumar ta ce wannan munafurci ne musamman idan da haka ya faru da wani marar kudi da zai sha suka da hantara.
Asali: Legit.ng