An Shiga Jimami Bayan Mutuwar Mahaifiyar Minista, Tinubu Ya Nuna Alhini
- An shiga jimami bayan rasuwar mahaifiyar Ministar kasuwanci da masana'antu a Najeriya, Dakta Doris Uzoka-Anite
- Shugaba Bola Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga iyalan marigayiyar Victoria Immaculata Uzoka inda ya yi mata addu'o'i na musamman
- Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa a jiya Litinin 8 ga watan Yulin 2024
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa Ministar kasuwanci da masana'antu kan rasuwar mahaifiyarta.
Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ne bayan rasuwar mahaifiyar Dakta Doris Uzoka-Anite mai suna Victoria Immaculata Uzoka.
Tinubu ya tura sakon ta'aziyya ga Ministarsa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa, Ajuri Ngelale ya fitar a shafin Facebook a jiya Litinin 8 ga watan Yulin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya jajantawa daukacin iyakan marigayiyar inda ya yi mata addu'ar samun rahama da kuma ba su hakuri kan wannan babban rashi.
Shugaban ya bukaci Ministar da sauran iyalanta da su dauki dangana saboda wannan babban rashi da aka yi musu.
Tinubu ya shawarci iyalan marigayiyar
Ya kuma bukace su da su samu kwarin guiwa da kuma koyi da kyawawan halayen marigayiyar da aka santa da su.
"Yayin da ya ke yi mata addu'ar samun rahama, Tinubu ya bukaci Ministar da iyalanta da su samu karfin guiwa game da zaman lafiya da taimakon al'umma da aka san marigayiyar da su."
- Cewar sanarwar
Ministar da ke kula da ma'aikatar masana'antu da kasuwanci da rasa mahaifiyarta ne Victoria Immaculata bayan ta sha fama da jinya na tsawon lokaci.
Buhari ya jajantawa Ministar Tinubu
A wani labarin mai kama da wannan mun kawo muku labarin rasuwar mahaifiyar Ministar harkokin ƴan sanda, Imaan Sulaiman-Ibrahim.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon ta'aziyya game da rasuwar mahaifiyar Ministar a jihar Nassarawa.
Buhari ya bayyana marigayiyar a matsayin mutumiyar kirki wacce kullum birninta shi ne tallafawa al'umma domin ci gaba.
Asali: Legit.ng