Alakar Jinsi: Gamayyar Matasa Sun Yi Zanga Zangar Kin LGBTQ da Matsin Rayuwa a Kano
- Matasa a Kano sun yi zanga zangar kin jinin auren jinsi da kokarin kawo cikawa cikin addini da al'ada ba
- Kamilu Hassan Abdullahi da ya jagoranci matasan Ciranci a ranar Litinin ya shaidawa Legit cewa ba za su lamunta ba
- Ya tunatar da jagororinsu a jiha da tarayya da malamai kan barranta kansu da wannan mugun nufi tun da wuri
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano- Matasa a jihar Kano sun fara barranta kansu da duk wani yunkuri na marawa auren jinsi da dangoginsa baya a kasar nan. Wannan na zuwa ne ana tsaka da batun sanya hannu kan yarjejeniyar SAMOA da bullar kungiyar cusawa matan Kano akida mu'amalar jinsi.
A safiyar yau gamayyar matasa a Ciranci da ke karamar hukumar Kumbotso su ka gudanar da zanga-zangar kin jinin lamarin mu'amalantar jinsi da akidar LGBTQ.
"Ba za mu amince ba," Matasan Kano
Gamayyar matasan Ciranci a karamar hukumar Kumbotso sun gudanar da zanga-zanga su na neman gwamnati da sauran wakilansu su takawa duk wani batu na auren jinsi burki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A hirarsa da Legit Hausa, Kamilu Hassan Abdullahi da ya jagoranci matasan ya ce ba za su zuba idanu a shigo da abin da zai saba addini ba.
"Duk wata saɗara, ko wani tsari, ko duk wani tsari, ko duk wani bayani da ya ke dauke da maganar ta wani abu da ya shafi harka ta neman maza, ko wani abu wanda ya sabawa addininmu na musulunci, ba ma goyon baya."
- Kamilu Hassan Abdullahi
Tuni dai aka fara jiyo wani talla daga ma'aikatar yada labarai a kafafen yada labarai da ke Kano ana barranta gwamnatin tarayya da batun auren jinsi a yarjeniyar SAMOA.
"Akwai matsaloli a Najeriya," Matasa
Gamayyar kungiyar matasan Ciranci ta bayyana cewa akwai tarin matsaloli da gwamnati ya kamata ta mayar da hankali a kansu.
Jagoran matasan, Kamilu Hassan Abdullahi ya bayyana cewa matsalolin tsaro da na tattalin arziki sun addabi jama'a.
Yayin zanga-zangar da su ka gudanar a ranar Litinin, sun nemi mahukunta su magance durkushewar Naira da matsalar tsaro a Arewa.
Kano: An dauki mataki kan akidar LGBTQ
A wani labarin kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta umarci hukumar hisbah ta bankado duk wasu kungiyoyi da ke cusa ra'ayin auren jinsi tsakanin jama'a.
Wannan na zuwa ne ana tsaka da tofin Allah tsine kan zargin cewa gwamnatin tarayya ta amince da batun auren jinsi a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng