'Yan Majalisa Sun Ba Gwamnan PDP Sabon Wa'adi Kan Kasafin Kudin 2024

'Yan Majalisa Sun Ba Gwamnan PDP Sabon Wa'adi Kan Kasafin Kudin 2024

  • Ƴan majalisar dokokin jihar Rivers ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule sun gudanar da zaman majalisa a ranar Litinin, 8 ga watan Yulin 2024
  • Ƴan majalisar masu biyayya ga ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike sun ba Gwamna Siminalayi Fubara wa'adi kan kasafin kuɗin shekarar 2024
  • Sun ba gwamnan wa'adin kwanaki bakwai domin ya sake gabatar musu da kasafin kuɗin a gaban majalisar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Rivers - Majalisar dokokin jihar Rivers ƙarƙashin jagorancin Martins Amaewhule ta ba Gwamna Siminalayi Fubara sabon wa'adi.

Majalisar ta ba Gwamna Simi Fubara wa'adin kwanaki bakwai domin ya sake gabatar mata da kasafin kuɗin shekarar 2024.

Majalisar dokokin Rivers ta ba Fubara sabon wa'adi
'Yan majalisar dokokin Rivers sun bukaci Gwamna Fubara ya gabatar da kasafin kudin 2024 Hoto: Sir Siminalayi Fubara, Martins Amaewhule
Asali: Facebook

Ƴan majalisa sun ba Gwamna Fubara wa'adi

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya nemi wata alfarma wajen mutanen Katsina kan matsalar tsaro

Umarnin ya biyo bayan zama na farko da ƴan majalisar masu biyayya ga ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, suka yi a ranar Litinin bayan wasu watanni, cewar rahoton tashar Channels tv.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaman ƴan majalisar shi ne na farko tun bayan da kotun ɗaukaka ƙara ta soke hukuncin babbar kotun jihar Rivers na hana ayyana kansu a matsayin ƴan majalisa.

Tsagin majalisar dokokin jihar mai biyayya ga Gwamna Fubara ƙarƙashin jagorancin Victor Oko-Jumbo na gudanar da na shi zaman na daban a birnin Portharcourt, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Tun da farko Gwamna Fubara ya gabatar da kasafin kuɗin ga ƴan majalisar masu biyayya a gare shi a lokacin da shugaban ma’aikatansa na yanzu Edison Ehie yake a matsayin shugaban majalisa.

Edison Ehie da sauran ƴan majalisar masu goyon bayan Fubara sun amince da ƙudirin kasafin kuɗin, kuma gwamnan ya sanya hannu kan ƙudirin dokar.

Kara karanta wannan

1446AH: Gwamnatin Borno ta ba da hutun sabuwar shekarar musulunci

Kotu ta kori ƴan majalisar Rivers

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun jihar Rivers mai zama a birnin Portharcourt ta hana ƴan majalisa da ke tsagin Nyesom Wike zama ko ayyana kansu a matsayin ƴan majalisar dokokin jihar.

Kotun ta bayar da umarnin wucin gadi ne a ƙarar da ƴan majalisa da ke goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara suka shigar gabanta tare da wasu mutum biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng