ASUU Ta Bayyana Abin da Zai Hana Ta Shiga Yajin Aiki a Fadin Najeriya

ASUU Ta Bayyana Abin da Zai Hana Ta Shiga Yajin Aiki a Fadin Najeriya

  • Ƙungiyar ASUU ta yi maganan kan yiwuwar shiga yajin aikin gama-gari a faɗin ƙasar nan cikin ƴan kwanakin da ke tafe
  • Shugaban ƙungiyar, Emmanuel Osodoke, ya bayyana cewa ƙungiyar ba za ta shiga yajin aiki ba idan gwamnati ta aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma
  • Farfesa Osodoke ya koka da cewa an ƙulla yarjejeniyoyin sama da shekara shida da suka gabata, amma har yanzu gwamnatin tarayya ta gaza aiwatar da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU), ta bayyana dalilin da zai sanya ta ƙi shiga yajin aikin gama-gari a faɗin ƙasar nan.

ASUU ta bayyana cewa ba za ta shiga yajin aiki ba idan gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma, nan da makonni biyu masu zuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan yiwa 'yan NYSC karin alawus

ASUU na shirin shiga yajin aiki a Najeriya
ASUU na son gwamnatin tarayya ta aiwatar da yarjeniyoyin da suka kulla Hoto: @ridoradeola
Asali: Twitter

ASUU na barazanar shiga yajin aiki

Shugaban ƙungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan dai za a iya tunawa, ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki saboda rashin aiwatar da yarjejeniyoyin da suka cimma da gwamnatin tarayya.

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman a ranar 26 ga watan Yuni ya gayyaci ƙungiyar domin tattaunawa kan matsalolin da suka dabaibaye jami’o’i da kuma hana shiga yajin aikin da suke shirin yi.

ASUU ta koka da gwamnatin tarayya

Shugaban na ASUU ya ce babu ɗaya daga cikin yarjejeniyoyin da aka ƙulla da gwamnatin tarayya da aka aiwatar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

"A taron da ministan ilimi ya kira. mun amince cewa bayan mako biyu za mu sake haɗuwa domin ganin ci gaban da gwamnati ta samu wajen aiwatar da yarjeniyoyin."

Kara karanta wannan

EFCC ta bankado makarkashiyar da ake kulla mata, hukumar ta aika da gargadi

“Za kuma mu ga abin da za mu yi na gaba idan gwamnati ta gaza aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma."

- Farfesa Emmanuel Osodoke

Ya ce an shafe sama da shekara shida da ƙulla yarjejeniyoyin kuma har yanzu gwamnati ba ta aiwatar da su ba.

ASUU na shirin shiga yajin aiki

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya (ASUU) ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta biya buƙatunta na inganta walwalar malaman jami'a.

Ƙungiyar ASUU ta yi gargaɗin cewa rashin cika waɗannan buƙatun ka iya sanyawa ta tsunduma cikin yajin aiki nan da makonni biyu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng