Auren Jinsi: Yadda Kururuwar Mutanen Kano Ya Dakile Yunkurin Kungiyar LGBTQ
- Ana tsaka da jimamin yadda gwamnatin tarayya da sanya hannu kan yarjejeniyar SAMOA, sai aka gano wata kungiya mai mugun nufi a Kano
- An gano kungiyar WISE ta na aikin yada manufar madigo da luwadi a cikin kauyukan Kano ta hanyar amfani da kungiyoyi masu zaman kansu
- Tuni ma'aikatar yada labarai da Kano da hukumar hisbah su ka bayyana matsayarsu kan kungiyar da irin wadannan kungiyoyi a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano- A yammacin Asabar da ta wuce, matasa musamman masu fafutukar kare hakkin dan Adam a Kano su ka gano wata kungiya ta Wise Nigeria Inititaive (WISE) mai kokarin yada alakar auren jinsi.
Daya daga irin wadannan matasa, kuma wanda ya shahara wajen ayyukan kare hakkin dan Adam, Musbahu L Hamza ya rubuta wasikar damuwa ga manema labarai da gwamnati.
A hirarsa da Legit Hausa, Musbahu L Hamza ya ce akwai fargaba da dama da su ka fada kamar guda uku, ciki har da;
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Karfin kungiyar WISE a Kano
Musbahu Hamza ya bayyana cewa a kwarya-kwaryar bincikensu, sun gano kungiyar ta na shiga kauyuka inda a nan ne ta ke yada akidar luwadi, madigo da sauya halitta.
Ya ce su na kokarin yin haka ne ta amfani da masu kananan kungiyoyi ana yaudarar jama'a da cewa za a basu tallafi, musmman mata da marayu.
2. Zargin alakar WISE da hisba
Daga fargabar da Musbahu ya ce sun fada shi ne yadda kungiyar ta yi wa jami'an hisba da KAROTA bita a Kano, wanda ke nuna cewa da shirinsu su ka shigo.
" Sai mu ke tunanin to Hisba ba su san su waye su ba ne? Kawai su ka amince da su har su ka kawo masu ziyara har su ka shirya masu bita da 'yan KAROTA?"
- Musbahu Hamza
3. Amfani da 'yan Kannywood
Matashi Musbahu Hamza da wasikarsa ta hasko ayyukan kungiyar WISE, ya bayyana cewa shi da sauran matasa na tsoron kungiyar ta WISE za ta rika amfani da 'yan kannywood wajen yada mugun nufi.
Ya ce amma sun zage damtse, kuma sai sun ga abin da ya turewa buzu nadi a kan batun, domin ba za su amince a lalata yaransu da su kansu ba.
Gwamnatin Kano ta yi martani
Bayan bullar labarin wata kungiya mai kokarin yada manufar luwadi, madigo, auren jinsi da sauya halitta a Kano, gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta dauki mataki.
An ji kwamishinan yada labarai na Kano, Baba Halilu Dantiye ya umarci hukumar hisba ta gudanar da bincike kan irin wadannan kungiyoyi a Kano.
Ya ce sam, gwamnati ba za ta amince a samar da wata kungiya ko amfani da wani daftari ko takarda wajen barin tasirin auren jinsi, madigo da luwadi a jihar.
Hisba ta bayyana matsayarta
Tuni hukumar kakkabe ayyukan badala a Kano ta hisba ta bayyana matsayarta kan kungiyar mai rajin yada akidar LGBTQ.
A sakon da shugaban hukumar, Shiekh Aminu Ibrahim Daurawa ya wallafa a shafinsa na Facebook ya ce za su yi binciken kwakkwafi kan lamarin.
"Ba za mu amince da badala ba," KSCF
Gamayyar kungiyoi masu zaman kansu a Kano ta ce tattaunawa ta yi nisa wajen gano su waye ke kokarin yada badala a Kano da sunan taimakawa mata.
Shugaban kungiyar, Ambasada Ibrahim Waiya, wanda shi ne shugaban sakatariyar kwamitin zaman lafiya na Kano ne ya shaidawa Legit hakan, inda ya ce za su tsaftace sauran kungiyoyi a jihar.
Kungiyar WISE ta rufe shafukanta
Bayan ca da aka yi wa kungiyar WISE mai rajin yada mummunar halayyar LGBTQ a Kano, Legit Hausa ta gano sun sauya abubuwan da ke shafukansa na sada zumunta.
Haka kuma shafin yanar gizo na kungiyar ba ya nuna komai, amma akwai sauran rubuce-rubucen kungiyar a shafukan LinkedIn kamar yadda za ku gani a kasa;
Jonathan ya yi watsi da auren jinsi
A baya kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi watsi batun auren jinsi ko kafa gidajen da ake luwadi da dangoginsa a kasar nan.
Wannaan ya jawo fushin kasashen yamma da ke ganin shugaban ya tauye hakkin 'yan adam, wanda ya jawo masa suka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng