Murna Yayin da Babban Basarake Ya Samu Motar Zinare, Bidiyo Ya Bayyana

Murna Yayin da Babban Basarake Ya Samu Motar Zinare, Bidiyo Ya Bayyana

  • An gabatar da sabuwar motar zinare ga Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, wanda ke nuna girmamawa da mutunta matsayinsa na sarkin gargajiya
  • Jigo a jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya sanya bidiyon motar a shafinsa na X watau Twitter inda ya bayyana muhimmancinta
  • Ƴan Najeriya da dama a shafukan sada zumunta sun yi martani kan wannan sabuwar motar da Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya samu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ile-Ife, jihar Osun - An gabatar da sabuwar motar zinare ga Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, Ojaja II.

An gabatar da motar ne ga basaraken na Yarabawa domin girmamawa da mutuntawa ga kujerar sarautar Ooni na Ife da yake riƙe da ita.

Kara karanta wannan

Sanusi II vs Aminu Ado: An fadi matsalar da Tinubu zai samu a Kano a siyasa

Ooni na Ife ya samu motar zinare
Ooni na Ife ya samu sabuwar motar zinare Hoto: @Naija_PR
Asali: Twitter

Ooni na Ife ya samu motar zinare

Kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito, jigo a jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya sanya bidiyon motar a shafinsa na X, @DeleMomodu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An kawo sabuwar motar zinare ga mai martaba Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, Ojaja II."
"Wannan motar na ƙara nuna matsayin Ooni mai daraja na basaraken gargajiya kuma Sarkin daular Yarabawa ta Ile-Ife."

- Dele Momodu

Yan Najeriya sun yi martani

Ƴan Najeriya sun yi amfani da shafukansu na sada zumunta na X domin mayar da martani kan wannan sabuwar motar ta Ooni na Ife.

@ogunleyeabayom ya rubuta:

"Kun je kuna ta kallon Bridgerton...Kowane ɗan Afirika har da fastoci yanzu su na kwaikwayon shi....Motar zinare ana cikin talauci."

@onekobo93 ya rubuta:

"Ina taya Sarkinmu murna, Allah ya sa wannan ya zama dalilin yin sarauta da farin ciki."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan yiwa 'yan NYSC karin alawus

@IamChukwuemeka ya rubuta:

"Wayyo, wannan abin mamaki ne, shugaba mai banbanci. Oni mai babban suna. Wannan abu ne mai kyau. Ran sarki ya daɗe."

@OmoYakubu1 ya rubuta:

"Duk domin ƙoƙarin zama kamar Sarauniya ko Sarkin Ingila. Mu riƙa yin abu irin na mu."

EFCC: Ooni na Ife na fargaba

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya bayyana fargabar cewa shugaban EFCC, Ola Olukoyede, na iya rasa aikinsa bayan ya bayyana shirinsa.

Basaraken mai daraja ta ɗaya ya yi wannan tsokaci ne a lokacin da yake mayar da martani kan dabarun aiki na hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ƙarƙashin jagorancin Olukoyede.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng