Kano: Abba Kabir Ya Dauki Mataki Kan Bullar Wata Kungiya Mai Tallata Alakar Jinsi

Kano: Abba Kabir Ya Dauki Mataki Kan Bullar Wata Kungiya Mai Tallata Alakar Jinsi

  • Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da bincike kan jita-jitar yaduwar wata kungiya mai tallata auren jinsi a jihar
  • Gwamnatin ta bukaci al'umma su kwantar da hankalinsu inda ta ce ba za ta taba barin irin wannan iya shege a jihar ba
  • Hakan ya biyo bayan bullar wata kungiya mai suna 'WISE' da ta dade tana tallata auren jinsi wurin fakewa da wasu ayyuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta yi martani kan bullar wata kungiya da ke tallata auren jinsi a jihar.

Gwamnatin jihar ta tabbatar da samun labarin kungiyar da ake kira 'WISE' inda ta ce ta kaddamar da bincike kan lamarin.

Abba Kabir ya kaddamar da bincike kan wata kungiya mai tallata auren jinsi
Gwamnatin jihar Kano ta fara bincike kan kungiyar 'WISE' da ake zargi da tallata auren jinsi. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Kano: Abba ya sha alwashin dakile matsalar

Hadimin gwamnan a bangaren sadarwa, Hassan Sani Tukur shi ya tabbatar da haka a shafinsa na X a yammacin yau Lahadi 7 ga watan Yulin 2024.

Kara karanta wannan

Basarake ya sha kunya bayan NDLEA ta kama shi da kayan maye, ta cafke wani a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hassan ya ce gwamnatin ta tabbatar da cewa ba za ta amince da duk wani iya shege makancin haka ba a jihar.

"Gwamnatin jihar Kano ta samu labarin wata kuniya da ke tallata auren jinsi tun jiya, tuni aka kaddamar da bincike kan lamarin."
"Muna mai tabbatarwa 'yan Kano cewa gwamnatinmu da ma wata gwamnatin mai zuwa a gaba ba za ta lamunci irin wannan iya shege ba."
"Muna mai kiran jama'a da su kwantar da hankalinsu, gwamnati ta dauki matakai kan lamarin."

- Hassan Sani Tukur

Ayyukan kungiyar WISE a jihar Kano

An tabbatar Kungiyar mai suna Women Initiative for Sustainable Empowerment and Equality (WISE) ta dade tana gudanar da ayyukanta a jihar, cewar Kano Times.

Kungiyar wacce ba ta gwamnati ba karkashin jagorancin Nnedinma Ulanmo tana da ofishinta mai lamba 239 a Jigirya Yankaba Kawaji, Bompai da ke jihar Kano.

Kara karanta wannan

Najeriya za ta samu bashin $150bn da halatta auren jinsi a yarjejeniyar Samoa?

Ayyukan kungiyar ya kara fitowa fili ne a 'yan kwanakin nan yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa.

Sheikh Gumi ya yi gargadi kan Samoa

A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Ahmed Gumi ya yi martani kan yarjejeniyar Samoa da gwamnati ta sanyawa hannu.

Sheikh Gumi ya yi gargadi kan lamarin inda ya ce manakisar Turawa ta wuce yadda mutane ke tunani musamman a wannan yanayi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.