"Ina Za Su Saka Kansu?" Atiku Ya Magantu Kan Karuwar Garkuwa Da Mutane

"Ina Za Su Saka Kansu?" Atiku Ya Magantu Kan Karuwar Garkuwa Da Mutane

  • Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya bayyana takaicin karuwar garkuwa da mutane
  • Ya bayyana rashin jin dadin yadda gwamnatin Bola Tinubu ke tafiyar da akalar kare rayuka da mutuncin yan jarida
  • Wannan na zuwa ne bayan sace tsohon shugaban kungiyar kwadago, wasu yan jaridu 2 da Alkaliya duk cikin mako guda

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaici kan halin da 'yan jarida su ka tsinci kansu a ciki. Atiku Abubakar, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a zaben da ya gabata a jam'iyyar PDP ya ce 'yan jarida haske ne ga al'umma.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon shugaban kungiyar NLC, an samu bayanai

Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa ya caccaki gwamnatin Tinubu kan karuwar garkuwa da mutane Hoto: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku Abubakar ya ce da takaici matuka yadda gwamnati da 'yan ta'adda su ke kokarin sako 'yan jarida a gaba.

"An shiga masifar rashin tsaro," Atiku

Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar ya caccaki gwamnati kan yadda ta ke kokarin kama wa tare da garkame 'yan jarida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da ya ce 'yan ta'adda sun hana mutanen kasar nan, ciki har da 'yan jarida a sakat.

Ya bayyana fargabar halin da 'yan kasa ke ciki bayan sace tsohon shugaban kungiyar ma'aikatan hasken wuta da gas, Takai Shamang mai shekaru 78. Atiku ya kara da cewa a yan kwanakin nan, an sace Alkaliya Janet Galadima Gimba da yaranta, duk da an sako yaran daga baya, sai kuma mahaifiyar mawaki Rarara.

Kara karanta wannan

An kama jagora a PDP, Atiku Abubakar ya zargi 'yan sanda da cin zarafin 'yan kasa

Ya ce lamurran da ke faruwa a 'yan kwanakin nan na nuna karara yadda gwamnati ta kasa tsare rayukan yan kasa, tare da neman a gaggauta ceto su, Vanguard ta wallafa.

An sace 'yan jarida a Najeriya

A wani labarin kun ji cewa wasu 'yan ta'adda sun kai hari jihar Kaduna inda su ka sace 'yan jarida gida biyu da iyalansu.

'Yan jaridan da ake sace sun hada da wakilin jaridar The Nation, AbdulGafar Alabelewe da na jaridar Blueprint, AbdulRaheem Aodu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.