"Yan Ta'adda na Barna a Tituna Fiye da Rashin Kyawun Hanyoyi," Shugaban Jami'a
- An gano yadda yan ta'adda da ayyukansu ke mummunar barazana daga rayukan 'yan Najeriya musamman matafiya
- Shugaban jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Enugu, Farfesa Aloysius Michaels Okolie ne ya shaidawa hukumar kare afkuwar hadurra matsalar
- Ya ce yanzu haka ta'addanci, ciki har da garkuwa da mutane da fashi da makami sun fi salwantar da rayukan 'yan kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Enugu - Shugaban jami'ar kimiyya da fasaha ta Enugu, Farfesa Aloysius Michaels Okolie ya gano abin da ya fi kashe 'yan Najeriya tsakanin 'yan ta'adda da rashin kyawun hanyoyi. Farfesa Okolie ya ce a yanzu haka, 'yan ta'adda sun fi lalatattun hanyoyin kasar nan kashe mutane.
Vanguard News ta tattaro cewa shugaban ya fadi haka ne lokacin da aka gabatarwa da jami'arsa sabon shugaban hukumar kare afkuwar hadurra yankin Ozalla.
"Garkuwa da mutane ya ta'azzara," Okolie
Shugaban jami'ar kimiyya da fasaha ta jihar Enugu, Farfesa Aloysius Michaels ya Okolie ya koka kan ta'azzarar ayyukan rashin tsaro a titunan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana haka ne a karshen mako, inda ya ce dawowar garkuwa da mutane da fashi da makami sun fi hallaka 'yan kasar nan kan munanan hanyoyin da ake da su.
Shugaban ya koka kan ƙaruwar kuncin rayuwa tsakanin 'yan kasa, wanda ke taka rawa wajen gudun wuce sa'a a tituna.
Ya ce matsin tattalin arziki a Najeriya babbar barazana ce ga rayuwar talakawan Najeriya, kuma rashin tsaro da munanan tituna na kara ta'azzara lamarin.
Farfesa Okolie ya yi alkawarin bayar da hadin kai ga hukumar FRSC wajen dakile yawaitar hadurra a yankin.
An sace fasto a hanyar zuwa jana'iza
A baya mun ruwaito cewa 'yan ta'adda sun sace wani malamin addinin musulunci a hanyarsa ta zuwa jihar Legas domin binne mahaifiyarsa.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kai hari kan motar da malamin addinin kiristan ke ciki tare da sace dukkanin fasinjojin.
Asali: Legit.ng