'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Shugaban Kungiyar NLC, an Samu Bayanai

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Tsohon Shugaban Kungiyar NLC, an Samu Bayanai

  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da wani tsohon shugaban kungiyar NLC daga gidansa da ke Kaduna
  • An ce 'yan bindigar sun sace Kwamared Takai Agang Shamang tsakanin karfe 7:30 na dare zuwa karfe 8:00 na daren ranar Juma’a
  • Daya daga cikin 'ya'yan Kwamared Takai ta ce hukumomi a jihar Kaduna na gudanar da bincike da kokarin ganin an kubutar da shi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Kaduna - An sace wani dattijo mai shekaru 79, Kwamared Takai Agang Shamang a gidansa da ke Bikini-Tsoraurang, Manchock, karamar hukumar Kaura a jihar Kaduna.

Misis Grace Yohannah Abbin, shugabar cibiyar bayar da agaji ta SARC a Kafancha, wadda daya ce daga cikin ‘ya’yan dattijon, ta tabbatar da faruwar lamarin a safiyar Lahadi.

Kara karanta wannan

Wuce gona da irin Isra'ila: Isra'ila ta farmaki makarantar majalisar dinkin duniya a Gaza

"Yan bindiga sun yi garkuwa da dattijo a jihar Kaduna
Masu garkuwa da mutane sun sace dattijo dan shekara 79 a karamar hukumar Kaura, jihar Kaduna. Hoto: Legit.ng
Asali: Original

'Yan bindiga sun sace dan shekara 79

Jarida Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da Kwamared Takai ne tsakanin karfe 7:30 na dare zuwa karfe 8:00 na daren ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Misis Grace, wasu gungun masu garkuwa da mutane ne suka shiga gidan mahaifinta inda suka kama shi da karfin tsiya suka tafi da shi.

An ce Kwamared Shamang, wanda ya yi fice wajen ayyukan agaji da sadaukar da kai ga fafutukar kare 'yancin 'yan kwadago, ya kasance mutum ne da ake mutuntawa.

An ce ya taba rike mukamin shugaban kungiyar kwadago NLC.

Al'umma na fatan dawowar dattijon

Misis Grace ta ce hukumomi a jihar Kaduna na gudanar da bincike kan lamarin, kuma ana ci gaba da kokarin ganin an kubutar da shi, in ji rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Katsina: 'Yan bindiga sun turo saƙon bidiyon mutanen da suka sace a Maidabino

Ta kara da cewa 'yan uwa, abokai, da masu fatan alheri na Kwamared Shamang suna nan suna fatan samun mafita mai kyau da kuma dawowar sa gida lafiya.

Har zuwa wallafa wannan rahoton ba a ji ta bakin kakakin rundunar ’yan sandan Kaduna, Mansir Hassan kan lamarin ba yayin da lambar wayarsa ta ki shiga.

'Yan bindiga sun kashe dan shekara 50

A wani labarin mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun kashe wani mutum mai shekaru 50 da dansa a wani hari da suka kawo masa a gidansa.

Yan bindigar sun kashe Alhaji Bello Danbuba mai shekaru 50 da karamin dansa , Aliyu, a kauyen Gandi dake a karamar hukumar Rabah jihar Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.