Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace diyar dan majalisa a Kano

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace diyar dan majalisa a Kano

Masu garkuwa da jama'a sun sace diyar dan majalisar dokoki a jihar Kano. A tsakar daren Asabar, miyagun sun sace diyar Alhaji Murtala Musa Kore mai wakiltar mazabar Dambatta.

Da misalin karfe 3 na daren, 'yan bindigar sun sace Juwairiyya bayan yunkurin sace mahaifinta da suka yi amma basu tarar da shi a gida ba. Dan uwanta Jamilu ne ya sanar da BBC.

Jamilu ya sanar da cewa mahaifinta yana cikin garin Kano lokacin da 'yan bindigar suka riskesu a gidansu da ke kauyen Kore na karamar Hukumar Dambatta.

Juwairiyya Murtala Musa, matashiya ce mai shekaru 17. Daliba ce da ke aji biyar a makarantar sakandiren gwamnati da ke Jogana. Ita ce diyar karshe a wurin dan majalisar mai wakiltar Dambatta.

"Mutane uku suka fara shigowa gidanmu amma babu wanda muka sani daga ciki kuma bamu san nawa bane suka tsaya a waje," cewar Jamilu.

"Mutanen sun ajiye abun hawarsu a nesa da gidanmu saboda ba iya hango shi muke ba."

Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace diyar dan majalisa a Kano
Da duminsa: Masu garkuwa da mutane sun sace diyar dan majalisa a Kano. Hoto daga Daily Nigerian
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yadda maza 10 suka yi gwajin 'gwaninta' a kaina - Matashiya mai shekaru 19

Matashi Jamilu ya ce da farko sun kama yayan mahaifinsu tare da dauresa duk a zatonsu shine Murtala Musa.

A wani labari na daban, ana zargin masu ta'adar garkuwa da mutane, sun yi awon gaba da wata jami'a ta 'yan sanda, ɗiyarta da kuma wasu mutum hudu a unguwar Janruwa da ke hanyar Patrick Yakowa a jihar Kaduna.

Wannan mummunan lamari kamar yadda wani bayar da shaida ya tabbatar ya bayyana cewa, ya auku ne da misalin karfe 10.00 na daren ranar Asabar da ta gabata.

Mutumin da yake bada shaidar; Babalola Mathew, ya ce 'yan ta'adda sun shigo unguwar cikin duhun dare inda suka afka wasu gidaje hudu salin alin cikin sanda.

Mista Mathew yace 'yan ta'addan sun yi awon gaba da mutum shida da suka hadar da babbar mace daya, wasu 'yan mata biyu, matasa biyu da kuma wani dattijo daya.

Yayin da manema labarai suka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Muhammadu Jalige, ya sha alwashin tattaro duk wasu bayanai game da lamarin daga babban jami'in dan sanda na Unguwar Janruwa.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel