Yan bindiga sun kashe wani dattijo mai shekaru 50 da dansa a Sokoto

Yan bindiga sun kashe wani dattijo mai shekaru 50 da dansa a Sokoto

- Wadansu yan bindiga da har yanzun ba a san ko suwaye ba sun kashe wani mutum mai shekaru 50 da dansa a wani hari da suka kawo masa a gidansa dake kauyen Gandi

- Yan bindigar sun kashe Alhaji Bello Danbuba mai shekaru 50 da karamin dansa , Aliyu, a kauyen Gandi dake a karamar hukumar Rabah jihar Sokoto

Legit.ng ta samu labarin cewa Kamfanin dillanci labarai ya rawaito cewa ana zargin barayin shanu ne suka zo domin satar masa rakoma a gidan nasa amma har suka kashe shi tare da dan nasa ba tare da sun dauki komai a gidan ba.

Mai magana da yawun yansandan jihar ya tabbatar da faruwar lamarin.

A wani labarin kuma, Kungiyar Kiristocin Najeriya ta yi Kira ga gwamnatin Tarayya da ta dai na fakewa da wadansu abubuwa domin boye gazawarsu kan kawo karshen rikicin Fulani Makiyaya da mazauna wasu garuruwa a fadin Kasa Najeriya.

Yan bindiga sun kashe wani dattijo mai shekaru 50 da dansa a Sokoto
Yan bindiga sun kashe wani dattijo mai shekaru 50 da dansa a Sokoto

KU KARANTA: Cututtuka 7 da zogale ke magani

Dayake hira da manema labarai a shirin da kungiyar ta keyi na fara yin wata taron gangami na kwana biyar a Abuja shugaban shirya taron kuma Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya Samson Ayokunle yace ayyukan Fulani a wasu sassan kasa Najeriya ya nuna cewa matsalar ya fi karfin gwamnati.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Bidiyon jirgin yaki

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel