An Kama Jagora a PDP, Atiku Abubakar Ya Zargi 'Yan Sanda Da Cin Zarafin 'Yan Kasa
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi rundunar yan sandan Najeriya da kin mutunta umarnin kotu
- Haka kuma ya zarge su da take hakkin dan Adam gami da cin zarafi a yadda su ke gudanar da ayyukansu
- Atiku ya bayyana haka ne ta cikin wata sanarwar dauke da sa hannun mashawarcinsa kan yada labarai, Paul Ibe a ranar Asabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya caccaki rundunar 'yan sandan Najeriya kan cin zarafin 'yan Najeriya. Haka kuma ya zargi jami'an 'yan sandan da kin bin umarnin kotu tare da take hakkin bil'adama a kasar nan.
Jaridar Nigerian Tribune ta tattaro cewa Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a martaninsa kan kama Yusuf Banki daga Abuja, tare da kai shi Maiduguri duknda umarnin kotu da ya haramta haka.
"Yan sanda su saki Yusuf Banki," Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya nemi yan sandan kasar nan su gaggauta sakin Yusuf Banki da ke tsare a hannunsu a jihar Borno. Atiku Abubakar ya nemi hakan ta cikin wata sanarwar dauke da sa hannun mashawarcinsa kan yada labarai, Paul Ibe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Punch ta wallafa cewa tsohon mataimakin shugaban kasar na ganin tsantsar rashin bin doka da oda na rundunar 'yan sanda.
A ranar 13 Yuni, 2024 ne Mai Shari'a M.A Madugu ya dakatar da yan sanda daga daukar wani mataki na kame ko takura wa Yusuf Banki da yan uwansa har sai kotu ta yanke hukunci.
Amma jami'an tsaro sun kama Yusuf Banki, wanda Atiku Abubakar ke ganin an yi amfani da karfi irin wanda ake gani a zamanin mulkin soja wajen kamen.
Yan sanda sun tabbatar da sace yan jarida
A wani labarin kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa 'yan ta'adda sun sace 'yan jarida gida biyu da iyalansu a jihar Kaduna.
'Yan ta'addan sun kai hari kauyen Donhonu a karamar hukumar Chikun inda suka fatattaki jama'a tare da sace 'yan jarida da 'yan uwansu.
Asali: Legit.ng