Sanusi II vs Aminu: Sheikh Dutsen Tanshi Ya Dauki Zafi Kan Rigimar Kano, Ya Fadi Matsayarsa
- Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Idris Abdul'aziz ya yi martani kan dambarwar sarautar jihar Kano
- Sheikh Idris ya ce duk wanda ya tube Sanusi II a sarauta ya cancanci yabo domin taimakon al'umma ya yi
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarauta tsakanin Aminu Ado Bayero da Muhammadu Sanusi II
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi ya yi tsokaci kan rigimar sarautar jihar Kano.
Shehin malamin daga jihar Bauchi ya soki Gwamna Abba Kabir kan mayar da Sanusi II kujerar saurata.
Sheikh Idris ya kushe matakin Abba Kabir
Malamin ya bayyana haka a wata hudubar Juma'a a karshen watan Yunin 2024 da aka yada a shafukan Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Idris ya ce da an bar masarautun guda hudu da yafi zama alheri da shawo kan matsalolin da ake fuskanta.
Malamin ya ce wannan ba daidai ba ne kuntatawa mutane domin biyan buƙatar kai a wannan zamani na dimukradiyya da ake ciki.
Kano: Sheikh Idris ya soki Sanusi II
"Wane irin ci gaba ne wannan kana azabtar da mutanenka saboda biyan buƙatar kanka a wannan lokaci na dimukradiyya."
"Mutane sai sun yi watanni biyu kafin su ga Sarki bayan rusa masarautu wanda a baya suna da ikon ganin sarki a kauyukansu."
"Ban taba ganin Ganduje ido da ido ba ko a waya, amma ina goyon bayan duk wanda ya yi dai-dai, ina ganin duk wanda ya tube Sanusi ya cancanci yabo."
"Idan muka yi duba a addinance, ni ba zan amince da wani yana kiran kansa malami ba yana yaudarar mutane."
"Saboda kawai ka karanta yaren Larabci na wasu watanni a Sudan ba zai tabbatar da kai a matsayin malami ba."
- Sheikh Idris Abdul-aziz
Farfesa ya yi tsokaci kan sarautar Kano
Kun ji cewa Farfesa Umar Labdo da ke Jami'ar Yusuf Maitama ya magantu kan rigimar da ake ci gaba da yi a jihar Kano kan sarauta.
Farfesa Labdo ya ce tun farko da sarakunan guda biyu sun yi koyi da kakansu, Muhammadu Sanusi I da hakan bai faru ba a jihar.
Asali: Legit.ng